M'Cheyne Bible Journey

Plano sa Pagbasa ng Bibliya — M'Cheyne Isang Taon

Sundin itong Bible Reading Plan sa apat na sipi sa isang araw—ang Lumang Tipan minsan at ang Bagong Tipan at Mga Awit dalawang beses sa isang taon.

365 Naayos ang isang taong plano
4 Apat na pagbabasa sa isang araw
180 Napiling araw
‹ Araw 180 / 365 ›
Bersyon

Pagkumpirma ng pagbabasa

Natapos mo ba itong M'Cheyne day?

Kumpirmahin ito upang markahan ang araw na ito na kumpleto sa iyong tsart ng pag-unlad ng M'Cheyne.

Pamilya · Lumang Tipan

여호수아 1

Buksan sa mambabasa →
Kabanata 1

The LORD Commands Joshua

1Bayan mutuwar Musa bawan Ubangiji, sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa ɗan Nun, mataimakin Musa,

2“Bawana Musa ya mutu. Yanzu sai ka tashi tare da mutanen nan duka, ku yi shirin ƙetare kogin Urdun zuwa cikin ƙasar da zan ba su Isra’ilawa.

3Zan ba ku duk ƙasar da za ku taka, kamar yadda na yi wa Musa alkawari.

4Ƙasar da ta kama daga hamada zuwa Lebanon, zuwa babban Kogin, wato, Kogin Yuferites, da dukan ƙasar Hittiyawa zuwa Bahar Rum, wajen yamma.

5Ba wanda zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai; ba zan taɓa rabuwa da kai ba; ba zan yashe ka ba.

6“Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, gama kai za ka bi da mutanen nan har su karɓi ƙasar da na yi wa kakanninsu alkawari zan ba su.

7Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, ka yi lura fa, ka yi biyayya da dokokin da bawana Musa ya ba ka; kada ka kauce ga bin dokokin ko hagu ko dama, domin ka yi nasara a duk, inda za ka je.

8Kada ka bar Littafin Dokokin nan yă rabu da bakinka, sai dai ka yi ta tunani game da shi dare da rana, don ka lura, ka yi duk abin da aka rubuta a ciki, ta haka ne za ka yi nasara cikin duk abin da za ka yi.

9Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”

Orders to Prepare to Cross the Jordan

10Saboda haka sai Yoshuwa ya umarci shugabannin mutane,

11“Ku ratsa cikin sansani, ku gaya wa mutane, ‘Ku shirya guzurinku. Nan da kwana uku za ku ƙetare Urdun a nan, don ku je ka mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ta zama taku.’ ”

The Promise of Reuben, Gad, and the Half-Tribe of Manasseh

12Amma Yoshuwa ya ce wa mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse,

13“Ku tuna da umarnin da Musa bawan Ubangiji ya yi muku. ‘Ubangiji Allahnku ya ba ku hutawa, ya kuma ba ku wannan ƙasa.’

14Matanku, da yaranku, da kuma dabbobinku za su kasance a ƙasar da Musa ya ba ku a gabashin Urdun, amma dole mayaƙanku, su yi shirin yaƙi su haye, su yi gaba tare da ’yan’uwanku, za ku taimaki ’yan’uwanku

15har sai lokacin da Ubangiji ya ba su hutawa, kamar yadda ya yi muku, kuma har sai su ma sun ƙwace ƙasar da Ubangiji Allahnku ya yi alkawari zai ba su. Bayan haka ne za ku koma ku mallaki ƙasarku, wadda Musa bawan Ubangiji ya ba ku a gabashin Urdun.”

16Sai suka amsa wa Yoshuwa suka ce, “Duk abin da ka ce mu yi, za mu yi. Duk inda kuma ka aike mu, za mu je.

17Kamar yadda muka yi wa Musa biyayya, haka za mu yi maka biyayya. Ubangiji Allahnka ya kasance tare da Musa.

18Duk wanda ya yi wa maganarka tawaye, ya ƙi yă yi biyayya da maganarka, ko da umarnin da ka ba shi, za a kashe shi. Ka dai ƙarfafa ka kuma yi ƙarfi hali!”

Pamilya · Bagong Tipan

시편 120, 121, 122

Buksan sa mambabasa →
Kabanata 120

Deliver Me from Lying Lips

1Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata,

2Ka cece ni, ya Ubangiji,

3Me zai yi maka,

4Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi,

5Kaitona da nake zama a Meshek,

6Da daɗewa na zauna

7Ni mutum ne mai salama;

Kabanata 121

Eyes Lifted to the Hills and the Lord Who Keeps

1Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai,

2Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,

3Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba,

4tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila

5Ubangiji yana tsaronka,

6rana ba za tă buge ka cikin yini ba

7Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa,

8Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka

Kabanata 122

Pray for the Peace of Jerusalem

1Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni,

2Ƙafafunmu suna tsaye

3An gina Urushalima kamar birnin

4A can ne kabilu suke haurawa,

5A can kursiyoyin shari’a yake tsaye,

6Ku yi addu’a don salamar Urushalima,

7Bari salama ta kasance a katangarki

8Saboda ’yan’uwana da kuma abokaina,

9Saboda gidan Ubangiji Allahnmu,

Lihim · OT / Mga Awit

이사야 61

Buksan sa mambabasa →
Kabanata 61

The Good News Proclaimed by the Anointed One

1Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina,

2don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji

3in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona,

4Za su sāke gina kufai na dā

5Baƙi za su yi kiwon garkunanki;

6Za a kuma kira ku firistocin Ubangiji,

7A maimakon kunyarsu

8“Gama ni, Ubangiji, ina ƙaunar adalci;

9Za a san da zuriyarsu a cikin al’ummai

10Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji;

11Gama kamar yadda ƙasa takan sa tsire-tsire su tohu

Lihim · Bagong Tipan

마태복음 9

Buksan sa mambabasa →
Kabanata 9

Jesus Heals a Paralytic

1Yesu ya shiga jirgin ruwa, ya ƙetare ya zo garinsa.

2Waɗansu mutane suka kawo masa wani shanyayye, kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Kada ka damu saurayi, an gafarta maka zunubanka.”

3Da jin wannan, waɗansu malaman dokoki suka ce wa juna, “Wannan mutum yana yin saɓo!”

4Sane da tunaninsu, Yesu ya ce, “Me ya sa kuke da mugun tunani a zuciyarku?

5Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya?’

6Amma don ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”

7Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gida.

8Da taron suka ga haka, sai suka cika da tsoro, suka yabi Allah wanda ya ba wa mutane irin ikon nan.

Jesus Calls Matthew the Tax Collector

9Da Yesu ya yi gaba daga wurin, sai ya ga wani mutum mai suna Mattiyu zaune a inda ake karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Mattiyu kuwa ya tashi ya bi shi.

10Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Mattiyu, masu karɓar haraji da yawa da kuma masu zunubi suka zo suka kuwa ci tare da shi da kuma almajiransa.

11Sa’ad da Farisiyawa suka ga haka, sai suka tambayi almajiransa suka ce, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji, da masu zunubi?”

12Da jin wannan, Yesu ya ce, “Ai, ba masu lafiya ba ne su bukatar likita, sai dai marasa lafiya.

13Amma ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba.’ Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”

A Question About Fasting

14Sai almajiran Yohanna suka zo suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa mu da Farisiyawa muke azumi, amma almajiranka ba sa yi?”

15Yesu ya amsa ya ce, “Yaya baƙin ango za su yi makoki yayinda yake tare da su? Lokaci yana zuwa da za a ɗauke ango daga gare su, sa’an nan za su yi azumi.

16“Ba mai yin faci da sabon ƙyalle a kan tsohuwar riga, gama facin zai kece rigar yă sa kecewar ma ta fi ta dā muni.

17Mutane kuma ba sa zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In suka yi haka, salkunan za su farfashe, ruwan inabin kuwa yă zube salkunan kuma su lalace. A’a, ai, sukan zuba sabon ruwan inabi ne a cikin sababbin salkuna, don a kiyaye dukan biyun.”

Jairus's Daughter and the Bleeding Woman

18Yayinda yake faɗin wannan, sai wani mai mulki ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Yanzu-yanzu diyata ta rasu. Amma ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, za tă kuwa rayu.”

19Yesu ya tashi ya tafi tare da shi, haka ma almajiransa.

20A daidai wannan lokaci sai ga wata mace wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini ta raɓo ta bayansa ta taɓa gefen rigarsa.

21Ta ce a ranta, “Ko da rigarsa ce kawai na taɓo, zan warke.”

22Yesu ya juya ya gan ta. Sai ya ce, “Kada ki damu diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke.” Nan take macen ta warke.

23Da Yesu ya shiga gidan mai mulkin ya ga masu busan sarewa da taro mai hayaniya,

24sai ya ce, “Ku ba da wuri. Ai, yarinyar ba tă mutu ba, tana barci ne.” Amma suka yi masa dariya.

25Bayan an fitar da taron waje, sai ya shiga ciki ya kama yarinyar a hannu, ta kuwa tashi.

26Labarin wannan kuwa ya bazu ko’ina a yankin.

Jesus Heals Two Blind Men

27Da Yesu ya fita daga can, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna kira, suna cewa, “Ka yi mana jinƙai, Ɗan Dawuda!”

28Da ya shiga cikin gida, sai makafin nan suka zo wurinsa, ya kuma tambaye su, “Kun gaskata cewa ina iya yin wannan?”

29Sa’an nan ya taɓa idanunsu ya ce, “Bisa ga bangaskiyarku a yi muku haka”;

30sai idanunsu suka buɗe. Yesu ya gargaɗe su sosai ya ce, “Ku lura kada wani yă san wani abu game da wannan.”

31Amma suka fita suka yi ta baza labari game da shi ko’ina a wannan yankin.

Jesus Heals a Man Unable to Speak

32Yayinda suke fitowa, sai aka kawo wa Yesu wani mutum mai aljani, da ba ya iya magana.

33Sa’ad da aka fitar da aljanin kuwa, sai beben ya yi magana. Taron suka yi mamaki suka ce, “Ba a taɓa ganin irin wannan abu a Isra’ila ba.”

34Amma Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.”

The Workers Are Few

35Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.

36Da ya ga taron mutane, sai ya ji tausayinsu, domin an wulaƙanta su ba su kuma da mai taimako, kamar tumaki marasa makiyayi.

37Sai ya ce wa almajiransa, “Girbi yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne.

38Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi, yă aiko da ma’aikata cikin gonarsa na girbi.”