FIL
FIL Filipino
M'Cheyne Bible Journey
Plano sa Pagbasa ng Bibliya — M'Cheyne Isang Taon
Sundin itong Bible Reading Plan sa apat na sipi sa isang araw—ang Lumang Tipan minsan at ang Bagong Tipan at Mga Awit dalawang beses sa isang taon.
KO Koreano
EN Ingles
CN Intsik
JP Hapon
PH mga wika sa Pilipinas
HI Hindi
BN Bengali
TA Tamil
TE Telugu
ML Malayalam
FA Persiyano
MY Burmese
NE Nepali
MR Marathi
KN Kannada
HA Hausa
YO Yoruba
SW Swahili
IG Igbo
ID Indones
PT Portuges
VI Biyetnames
AR Arabe
RU Ruso
UK Ukrainiano
RO Rumano
IT Italyano
FI Pinlandes
TO Tongan
HR Kroatyano
SR Serbiano
TR Turko
HU Unggaro
PL Polako
SK Eslobako
LA Latin
NL Olandes
CS Tseko
FR Pranses
ES Espanyol
DE Aleman
OT Iba pang mga wika
Pagkumpirma ng pagbabasa
Natapos mo ba itong M'Cheyne day?
Kumpirmahin ito upang markahan ang araw na ito na kumpleto sa iyong tsart ng pag-unlad ng M'Cheyne.
여호수아 2
Rahab Hides the Spies
1Sai Yoshuwa ɗan Nun ya aika ’yan leƙen asiri guda biyu a ɓoye daga Shittim ya ce, “Ku je ku duba, ku ga yadda wurin yake, musamman Yeriko.” Sai suka je suka shiga gidan wata karuwa mai suna Rahab, suka sauka a can.
2Aka gaya wa sarkin Yeriko cewa, “Ji fa, waɗansu Isra’ilawa sun shigo nan da dare don su leƙi asirin ƙasar.”
3Saboda haka sai sarki ya aika wannan saƙo zuwa ga Rahab, “Ki fito da mutanen da suka zo suka sauka a gidanki, gama sun zo su leƙi asirin ƙasar ne gaba ɗaya.”
4Amma matar ta ɓoye mutanen nan biyu. Ta ce, “I, mutanen sun zo wurina, amma ban san daga ina suka zo ba,
5da yamma kuwa, kafin a rufe ƙofar gari sai mutanen suka tafi. Ban san hanyar da suka bi ba, ku yi sauri ku bi su. Mai yiwuwa ku same su.”
6(Amma ta kai su saman rufin ɗaki ta ɓoye su a ƙarƙashin karan rama da ta baza a rufin ɗaki.)
7Sai mutanen garin suka kama hanyar Urdun don su nemi ’yan leƙen asirin, daga fitar su sai aka rufe ƙofar garin.
The Oath of Rahab and the Spies
8Kafin ’yan leƙen asirin su kwanta, sai ta tafi wurinsu a bisa rufin ɗakin
9ta ce musu, “Na sani Ubangiji ya riga ya ba ku ƙasan nan, tsoronku kuma ya kama mu har zukatan mazaunan ƙasar duka sun narke saboda ku.
10Mun ji yadda Ubangiji ya busar da ruwan Jan Teku domin ku lokacin da kuka fito daga ƙasar Masar, da kuma abin da kuka yi wa Sihon da Og, sarakunan nan biyu na Amoriyawa gabas da Urdun, waɗanda kuka hallaka su sarai.
11Da muka ji labarin, duk sai zuciyar kowa ta narke, kowa ya karaya saboda ku, gama Ubangiji Allahnku shi ne Allah na sama da ƙasa.
12Yanzu ina roƙonku ku rantse mini da Ubangiji cewa za ku yi wa iyalina alheri kamar yadda na yi muku alheri. Ku ba ni ƙwaƙƙwarar shaida cewa
13za ku ceci rayukan mahaifina da mahaifiyata, da ’yan’uwana maza da mata, da duk waɗanda suke nasu, za ku cece mu daga mutuwa.”
14Mutanen suka tabbatar mata suka ce, “Ranmu a bakin ranki! In ba ki faɗa wa kowa abin da ya kawo mu ba, za mu yi miki alheri da aminci lokacin da Ubangiji ya ba mu ƙasar.”
15Sai ta zura igiya ta taga suka bi, domin gidan da take yana haɗe da katangar birnin.
16Ta ce musu, “Ku tafi cikin tuddan ƙasar don kada mutanen sarki su same ku. Ku ɓuya a can na kwana uku, har sai masu nemanku su komo, sa’an nan ku kama hanyarku.”
17Mutanen suka ce mata, “Rantsuwar da kika sa muka yi, ba za tă yi amfani ba
18sai in kin ɗaura jan ƙyalle a tagar da kika zura mu, kuma sai in kin kawo mahaifinki da mahaifiyarki, da ’yan’uwanki, da dukan iyalinki cikin gidanki.
19In wani ya fita kan hanya, alhakin jininsa yă kasance a kansa; ba ruwanmu. Amma in aka taɓa wani da yake cikin gidanki tare da ke, alhakin jininsa yana kanmu.
20In kika tone mana asiri, za mu karya alkawarin da kika sa muka yi.”
21Ta ce, “Na yarda! Bari yă zama yadda kuka ce.”
The Spies Return and Report
22Sai suka tafi, suka shiga cikin tuddai, suka yi zamansu a can kwana uku har masu nemansu suka koma, gama masu nemansu suka yi ta nema ko’ina a hanyar, amma ba su sami kowa ba.
23Sa’an nan mutanen nan biyu, ’yan leƙen asiri suka sauka daga tuddai suka haye kogi zuwa wurin Yoshuwa ɗan Nun, suka gaya masa duk abin da ya faru da su.
24Suka ce wa Yoshuwa, “Ba shakka Ubangiji ya ba mu ƙasan nan duka, tana hannunmu, mutane can duk sun narke da tsoro saboda mu.”
시편 123, 124, 125
Eyes Lifted in Hope of Mercy
1Na tā da idanuna gare ka,
2Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu,
3Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai,
4Mun jimre da wulaƙanci
Salvation like a Bird Escaped from the Snare
1Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba,
2da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba
3sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu,
4da rigyawa ta kwashe mu,
5Da ruwa mai hauka
6Yabo ya tabbata ga Ubangiji,
7Mun tsira kamar tsuntsu
8Taimakonmu yana a sunan Ubangiji,
The Lord Who Surrounds and Keeps like the Mountains
1Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona,
2Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima,
3Sandar mulkin mugaye ba zai ci gaba da kasance
4Ka yi alheri, ya Ubangiji, ga waɗanda suke nagartattu,
5Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyi
이사야 62
Zion's New Name and the Unceasing Watchmen
1Saboda Sihiyona ba zan yi shiru ba,
2Al’ummai za su ga adalcinki,
3Za ki zama rawanin daraja a hannun Ubangiji,
4Ba za a ƙara ce da ke Yasasshiya ba,
5Kamar yadda saurayi kan auri yarinya,
6Na sa matsara a kan katangarki, ya Urushalima;
7kuma kada ku ba shi hutu sai ya kafa Urushalima
8Ubangiji ya rantse da hannunsa na dama
9amma waɗanda suka girbe shi za su ci shi
10Ku wuce, ku wuce ƙofofi!
11Ubangiji ya yi shela
12Za a ce da shi Tsattsarkar Mutane,
마태복음 10
Jesus Sends Out the Twelve Apostles
1Sai ya kira almajiransa goma sha biyu wurinsa ya kuma ba su iko su fitar aljanu, su kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
2Ga sunayen manzannin nan goma sha biyu,
3Filibus da Bartolomeyu;
4Siman Zilot da kuma Yahuda Iskariyot wanda ya bashe Yesu.
5Waɗannan sha biyun ne Yesu ya aika da umarni cewa, “Kada ku je cikin Al’ummai, ko kuwa ku shiga wani garin Samariyawa.
6A maimakon haka ku je wajen ɓatattun tumakin Isra’ila.
7Sa’ad da kuke tafiya, ku yi wa’azi, kuna cewa, ‘Mulkin sama ya kusato.’
8Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta.
9“Kada ku riƙe wata zinariya ko azurfa ko jan ƙarfe a aljihunanku,
10kada ku ɗauki jaka don tafiya, ko ƙarin riga, ko takalma ko sanda; domin ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.
11Kowane gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a wurin, ku kuma zauna a gidansa har sai kun tashi.
12Da shigarku gidan, ku yi gaisuwa.
13In gidan na kirki ne, bari salamarku ta zauna a kansa; in kuwa ba mai kirki ba, salamarku ta komo muku.
14Duk wanda ya ƙi marabtarku ko ya ƙi sauraron kalmominku, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita gidan ko garin.
15Gaskiya nake gaya muku, za a fi jin tausayin Sodom da Gomorra a ranar shari’a fiye da wannan gari.
Coming Persecutions Foretold
16“Ina aikan ku kamar tumaki a cikin kyarketai. Saboda haka ku zama masu wayo kamar macizai, kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.
17Ku yi hankali da mutane; za su miƙa ku ga majalisa su kuma yi muku bulala a majami’unsu.
18Saboda ni, za a ja ku zuwa gaban gwamnoni da gaban sarakuna domin ku ba da shaida a gabansu, da kuma ga Al’ummai.
19Amma sa’ad da suka kama ku, kada ku damu game da abin da za ku faɗa ko kuwa yadda za ku faɗe shi. A lokacin za a ba ku abin da za ku faɗa,
20gama ba ku ba ne kuke magana, amma Ruhun Ubanku ne yake magana ta wurinku.
21“Ɗan’uwa zai ci amanar ɗan’uwansa, a kuma kashe shi, Uba ma zai yi haka da ɗansa; ’ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.
22Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto.
23Sa’ad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Isra’ila, Ɗan Mutum zai zo.
24“Ɗalibi ba ya fin malaminsa, haka ma, bawa ba ya fin maigidansa.
25Ya isa wa ɗalibi yă zama kamar malaminsa, haka ma bawa kamar maigidansa. In har an kira wanda yake kan gida Be’elzebub, me za su ce game da mutanen gidansa?
Fear Him Who Is to Be Feared
26“Saboda haka kada ku ji tsoronsu. Ba abin da yake a rufe da ba za a tone ba, ko kuwa a ɓoye da ba za a bayyana ba.
27Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki.
28Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta.
29Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku.
30Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su.
31Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.
32“Duk wanda ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin sama.
33Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama.
Not Peace, but a Sword
34“Kada fa ku ɗauka na zo ne don in kawo salama a duniya. A’a, ban zo don in kawo salama ba, sai dai takobi.
35Gama na zo ne in sa,
36abokan gāban mutum, za su zama mutanen gidansa ne.’
37“Duk wanda ya fi ƙaunar mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; duk kuwa wanda yake ƙaunar ɗansa ko diyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba;
38duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yă zama nawa ba.
39Duk mai son adana ransa zai rasa shi, duk wanda kuwa ya rasa ransa saboda ni zai same shi.
Rewards for Receiving a Disciple
40“Wanda ya karɓe ku, ya karɓe ni ne, wanda kuma ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.
41Duk wanda ya karɓi annabi don shi annabi ne, zai sami ladar annabi, duk kuwa wanda ya karɓi mutum mai adalci don shi mai adalci ne, zai sami ladar mai adalci.
42In kuma wani ya ba wa ɗaya daga cikin ƙananan nan ko da kwaf ruwan sanyi ne kan shi almajirina ne, gaskiya nake gaya muku, ba shakka ba zai rasa ladarsa ba.”