KO
KO 한국어
EN 영어
CN 중국어
JP 일본어
PH 필리핀어권
HI 힌디어
BN 벵골어
TA 타밀어
TE 텔루구어
ML 말라얄람어
FA 페르시아어
MY 버마어
NE 네팔어
MR 마라티어
KN 칸나다어
HA 하우사어
YO 요루바어
SW 스와힐리어
IG 이그보어
ID 인도네시아어
PT 포르투갈어
VI 베트남어
AR 아랍어
RU 러시아어
UK 우크라이나어
RO 루마니아어
IT 이탈리아어
FI 핀란드어
TO 통가어
HR 크로아티아어
SR 세르비아어
TR 튀르키예어
HU 헝가리어
PL 폴란드어
SK 슬로바키아어
LA 라틴어
NL 네덜란드어
CS 체코어
FR 프랑스어
ES 스페인어
DE 독일어
OT 기타 언어
통독 확인
이 일차의 맥체인 본문을 완료했나요?
확인 버튼을 누르면 마이페이지 맥체인 진도표에 완료로 기록됩니다.
역대하 36
The Reigns of Jehoahaz and Jehoiakim
1Sai mutanen ƙasar suka ɗauki Yehoyahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki a Urushalima yă gāji mahaifinsa.
2Yehoyahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima wata uku.
3Sarkin Masar ya tumɓuke shi a Urushalima, ya tilasta Yahuda su biya haraji talenti ɗari na azurfa da kuma talentin zinariya.
4Sarkin Masar ya naɗa Eliyakim, ɗan’uwan Yehoyahaz, sarki a bisa Yahuda da kuma Urushalima, ya kuma canja sunan Eliyakim zuwa Yehohiyakim. Amma Neko ya ɗauki Yehoyahaz ɗan’uwan Eliyakim ya kai Masar.
5Yehohiyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnsa.
6Nebukadnezzar sarkin Babilon ya hauro ya kara da shi. Ya kama shi, ya daure da sarƙoƙin tagulla, ya kuma kai shi Babilon.
7Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kuma kwaso kayayyaki daga haikalin Ubangiji ya sa su a haikalinsa a can.
8Sauran ayyukan mulkin Yehohiyakim, ayyukan banƙyamar da ya aikata da dukan abubuwan da aka same shi da su, suna a rubuce cikin littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda. Sai Yehohiyacin ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
The Reigns of Jehoiachin and Zedekiah
9Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima wata uku da kwana goma. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji.
10Da bazara, Sarki Nebukadnezzar ya aika a kawo Yehohiyacin, aka kuma kawo shi Babilon, tare da kayayyaki masu daraja daga haikalin Ubangiji, sai Sarki Nebukadnezzar ya naɗa kawunsa Zedekiya, sarki a bisa Yahuda da Urushalima.
11Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya.
12Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnsa kuma bai ƙasƙantar da kansa a gaban Irmiya annabi, wanda ya yi magana kalmar Ubangiji ba.
13Ya tayar wa Sarki Nebukadnezzar, wanda ya sa ya yi rantsuwa da sunan Allah. Ya zama mai kunnen ƙashi da kuma taurin zuciya, bai kuwa juye ga Ubangiji, Allah na Isra’ila ba.
14Bugu da ƙari, dukan shugabannin firistoci da mutane suka ƙara zama marasa aminci, suna bin dukan abubuwan banƙyama na al’ummai, suka ƙazantar da haikalin Ubangiji, wanda ya tsarkake a Urushalima.
15Sai Ubangiji Allah na kakanninsu, ya yi ta aika da magana gare su ta wurin ’yan saƙonsa sau da sau, domin ya ji tausayi mutanensa da mazauninsa.
16Amma suka yi wa ’yan saƙon Allah ba’a, suka rena maganarsa, suka yi wa annabawansa dariyar reni, har sai da fushin Ubangiji ya tasar a kan mutanensa babu makawa.
The Fall of Jerusalem and the Babylonian Exile
17Ya bashe su ga sarkin Babiloniyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a wuri mai tsarki, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka ga Nebukadnezzar.
18Nebukadnezzar ya kwashe dukan kayayyaki daga haikalin Allah, babba da ƙarami, da ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin sarki da na fadawansa zuwa Babilon.
19Suka cinna wa haikalin Allah wuta, suka rurrushe katangar Urushalima; suka ƙone dukan fada, suka kuma lalace kome mai amfani da yake can.
20Waɗanda ba a kashe ba kuwa Nebukadnezzar ya kwashe su, ya kai Babilon, suka zama bayinsa da na ’ya’yansa maza har zuwa kahuwar mulkin Farisa.
21Ƙasar ta more hutun Asabbacinta; a dukan lokacin zamanta kango ta huta, har sai da shekaru saba’in nan suka cika bisa ga maganar Ubangiji da Irmiya ya faɗi.
The Decree of Cyrus for the Return
22Don a cika maganar da Ubangiji ya yi ta wurin Irmiya, a shekara farko ta Sairus sarkin Farisa, sai Ubangiji ya motsa zuciyar Sairus na Farisa don yă yi shela a dukan masarautarsa, ya kuma sa shi a rubuce cewa,
23“Ga abin da Sairus sarkin Farisa ya ce,
요한계시록 22
The River of the Water of Life and the Tree of Life
1Sai mala’ikan ya nuna mini kogin ruwan rai, mai ƙyalli kamar madubi, yana gangarawa daga kursiyin Allah da na Ɗan Ragon,
2yana bin tsakiyar babban titi na birnin. A kowane gefen kogin akwai itacen rai mai ba da ’ya’ya goma sha biyu, yana ba da ’ya’yansa kowane wata. Ganyayen itacen kuwa saboda warkar da al’ummai ne.
3Ba za a ƙara samun la’ana ba. Kursiyin Allah da na Ɗan Ragon zai kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa hidima.
4Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu.
5Ba za a ƙara yin dare ba. Ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su kuwa yi mulki har abada abadin.
The Promise of Coming Soon and the Warning
6Mala’ikan ya ce mini, “Waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma. Ubangiji, Allahn ruhohin annabawa, ya aiki mala’ikansa, don yă nuna wa bayinsa abubuwan da za su faru nan ba da daɗewa ba.”
7“Ga shi! Ina zuwa da wuri! Mai albarka ne wanda yake kiyaye kalmomin annabcin da suke cikin wannan littafi.”
8Ni, Yohanna, na ji, na kuma ga abubuwan nan. Kuma sa’ad da na ji, na kuma gan su, sai na fāɗi a ƙasa a gaban mala’ikan da yake nuna mini su, don in yi sujada.
9Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da ’yan’uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye kalmomin wannan littafi. Allah za ka yi wa sujada!”
10Sa’an nan ya gaya mini cewa, “Kada ka rufe kalmomin annabcin littafin nan, domin lokaci ya yi kusa.
11Duk mai yin laifi yă ci gaba da yin laifi; duk mai aikata ƙazanta yă ci gaba da aikata ƙazanta. Duk mai aikata abin da yake daidai, yă ci gaba da aikata abin da yake daidai. Kuma duk wanda yake mai tsarki, yă ci gaba da yin abin da yake da tsarki.”
12“Ga shi, ina zuwa da wuri! Ladan da zan bayar yana tare da ni, kuma zan ba wa kowa gwargwadon abin da ya yi.
13Ni ne Alfa da kuma Omega, na Fari da kuma na Baya, Farko da kuma Ƙarshe.
14“Masu albarka ne waɗanda suka wanke tufafinsu, don su sami izinin ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta ƙofofi.
15Waɗanda suke waje kuwa karnuka ne, masu sihiri, masu fasikanci, masu kisankai, masu bautar gumaka, da duk wanda yake ƙaunar ƙarya yake kuma aikata ta.
The Final Testimony and the Plea for the Lord
16“Ni, Yesu, na aiko mala’ikana ya ba ka wannan shaida saboda ikkilisiyoyi. Ni ne Tushe da kuma Zuriyar Dawuda, da kuma Tauraron Asubahi mai haske.”
17Ruhu da kuma amarya suna cewa, “Zo!” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo!” Duk mai jin ƙishirwa, yă zo; duk mai bukata kuma, yă ɗibi ruwan rai kyauta.
18Ina yin wa duk wanda ya ji kalmomin annabcin wannan littafi gargaɗi. Duk wanda ya ƙara wani abu a kansu, Allah zai ƙara masa annoban da aka bayyana a littafin nan.
19Duk wanda kuma ya yi ragi a kalmomi daga littafin annabcin nan, Allah zai ɗauke rabonsa na itacen rai da kuma na birnin nan mai tsarki, waɗanda aka bayyana a littafin nan.
20Shi da ya shaida waɗannan abubuwa ya ce, “I, ina zuwa da wuri.”
21Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da mutanen Allah. Amin.
말라기 4
The Day of the Lord and the Sun of Righteousness
1“Tabbatacce rana tana zuwa; za tă yi ƙuna kamar wutar maƙera. Dukan masu girman kai da kowane mai aikata mugunta zai zama ciyawa, wannan rana mai zuwa za tă ƙone su. Babu saiwa ko reshen da za a bar musu,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
2Amma ku da kuke girmama sunana, ranar adalci za tă fito tare da warkarwa a fikafikanta. Za ku kuwa fita kuna tsalle kamar ’yan maruƙan da aka sake daga garke.
3Sa’an nan za ku tattake mugaye; za su zama toka a ƙarƙashin tafin ƙafafunku a ranar da zan aikata waɗannan abubuwa, in ji Ubangiji Maɗaukaki.
I Will Send Elijah
4“Ku tuna da dokar bawana Musa, ƙa’idodi da dokokin da na ba shi a Horeb domin dukan Isra’ila.
5“Ga shi, zan aika muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji tă zo.
6Zai juye zukatan iyaye ga ’ya’yansu, zukatan ’ya’ya kuma ga iyayensu; in ba haka ba zan bugi ƙasar da hallaka gaba ɗaya.”
요한복음 21
Jesus Appears at the Sea of Tiberias
1Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya. Ga yadda ya faru.
2Siman Bitrus, Toma (wanda ake kira Didaimus), Natanayel daga Kana ta Galili, ’ya’yan Zebedi maza, da kuma waɗansu almajirai guda biyu suna tare.
3Sai Siman Bitrus ya ce musu, “Za ni kamun kifi,” suka ce, “Za mu tafi tare da kai.” Saboda haka suka fita suka shiga jirgin ruwa, amma a daren nan ba su kama kome ba.
4Da sassafe, sai ga Yesu tsaye a gaci, amma almajiran ba su gane cewa Yesu ne ba.
5Sai ya ce musu, “Abokai, kuna da kifi kuwa?”
6Ya ce musu, “Ku jefa abin kamun kifinku dama da jirgin ruwan, za ku samu.” Da suka yi haka, sai suka kāsa jawo abin kamun kifin saboda yawan kifi.
7Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, “Ai, Ubangiji ne,” sai ya yafa mayafinsa (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan.
8Sauran almajiran kuwa suka bi shi cikin jirgin ruwan, janye da abin kamun kifin cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, wajen yadi ɗari ne.
9Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma ’yan burodi.
10Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.”
11Sai Siman Bitrus ya hau ya jawo abin kamun kifin gaci. Ya cika da manyan kifi, 153, amma duk da yawansun nan abin kamun kifin bai tsintsinke ba.
12Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Ba wani daga cikin almajiran da ya yi karambanin tambayarsa, “Wane ne kai?” Sun san cewa Ubangiji ne.
13Yesu ya zo, ya ɗauki burodin ya ba su, haka kuma kifin.
14Wannan fa shi ne sau na uku da Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa bayan an tashe shi daga matattu.
Jesus Restores Peter
15Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?”
16Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?”
17Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?”
18Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.”
19Yesu ya faɗi wannan ne, don yă nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yă ɗaukaka Allah. Sa’an nan ya ce masa, “Bi ni!”
20Bitrus ya juya ya ga cewa almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. (Wannan ne ya jingina a jikin Yesu sa’ad da suke cin abincin yamman nan da ya ce, “Ubangiji wane ne zai bashe ka?”)
21Da Bitrus ya gan shi sai ya ce, “Ubangiji, wannan fa?”
22Yesu ya amsa ya ce, “Idan na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai bi ni.”
23Saboda wannan, jita-jita ta bazu a cikin ’yan’uwa cewa wannan almajirin ba zai mutu ba. Amma fa Yesu bai ce ba zai mutu ba; shi dai ya ce, “In na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki?”
24Wannan shi ne almajirin da ya ba da shaida a kan waɗannan abubuwa ya kuma rubuta su. Mun san cewa shaidarsa gaskiya ce.
25Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za tă sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba.