麦琴圣经旅程

麦琴一年读经计划

每天四处经文,一年读旧约一遍、新约和诗篇两遍。

365 一年固定读经表
4 每天四处经文
89 所选天数
‹ 第89天 / 共365天 ›
译本

读经确认

你完成了这一天的麦琴读经吗?

点击确认后,会在我的页面麦琴进度表中记录为已完成。

家庭崇拜·旧约

레위기 1

打开经文 →
第1章

Laws for Burnt Offerings

1Ubangiji ya kira Musa ya yi masa magana daga cikin Tentin Sujada ya ce,

2“Yi magana da Isra’ilawa ka ce musu, ‘Duk sa’ad da waninku ya kawo hadaya ga Ubangiji, ku kawo hadayarku ta dabba daga garkenku ta shanu ko kuwa daga tumakinku.

3“ ‘In hadaya ta ƙonawar daga shanu ne, sai yă miƙa namiji marar lahani. Dole yă kawo shi a ƙofar Tentin Sujada don yă zama yardajje ga Ubangiji.

4Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya ta ƙonawar, za a kuwa karɓa a madadinsa don a yi kafara dominsa.

5Zai yanka ɗan bijimin a gaban Ubangiji, Haruna kuwa da ’ya’yansa maza firist, za su kawo jinin su kuma yafa shi a kan bagaden a kowane gefe a mashigin Tentin Sujada.

6Zai feɗe hadaya ta ƙonawar, yă yayyanka shi gunduwa-gunduwa.

7’Ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci za su hura wuta a bagade, su kuma shirya itace a kan wutar.

8Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci za su shirya gunduwa-gunduwar haɗe da kan da kuma kitsen a kan itace mai cin wuta wanda yake a kan bagaden.

9Zai wanke kayan cikin da kuma ƙafafun da ruwa, firist ɗin kuwa zai ƙone dukan waɗannan a kan bagade. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

Burnt Offering from the Flock

10“ ‘In hadaya ta ƙonawar daga garke ne, ko na tumaki, ko na awaki, zai miƙa namiji ne marar lahani.

11Zai yanka shi a gefen arewa na bagaden a gaban Ubangiji, ’ya’yan Haruna firistoci kuwa za su yayyafa jinin dabbar a bagaden a kowane gefe.

12Zai yanka shi gunduwa-gunduwa, firist kuwa zai shirya su haɗe da kan, da kuma kitsen a kan itace mai cin wutar da yake a kan bagade.

13Zai wanke kayan cikin da kuma ƙafafun da ruwa, firist ɗin kuwa zai ƙone dukan waɗannan a kan bagade. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

Burnt Offering of Birds

14“ ‘In hadaya ga Ubangiji ɗin, hadaya ta ƙonawa ta tsuntsaye ce, zai miƙa kurciya ko ’yar tattabara.

15Firist zai kawo ta bagade, yă murɗe wuyan tsuntsun yă ƙone shi a kan bagade; zai tsiyaye jininsa tsuntsun a gefen bagaden.

16Amma zai ɗauki kayan cikin tsuntsun da gashin yă zubar da su a gefen bagaden a wajen gabas a wurin zuba toka.

17Zai tsaga shi biyu a tsaka, amma ba zai raba shi ba. Firist ɗin zai ɗibiya shi a bisa itacen da yake bisa bagaden, yă ƙone shi. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

家庭崇拜·新约

요한복음 20

打开经文 →
第20章

The Empty Tomb

1Da sassafe a ranar farko ta mako, tun da sauran duhu, Maryamu Magdalin ta tafi kabarin ta kuwa tarar an kawar da dutsen daga bakin kabarin.

2Sai ta zo da gudu wajen Siman Bitrus da ɗayan almajirin, wanda Yesu yake ƙauna, ta ce, “Sun ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuma san inda suka sa shi ba!”

3Sai Bitrus da almajirin nan suka nufi kabarin.

4Dukansu biyu suna gudu, amma ɗayan almajirin ya tsere wa Bitrus ya kuma fara kai kabarin.

5Ya sunkuya ya duba ciki ya ga ƙyallayen lilin ne kwance a can amma bai shiga ba.

6Sa’an nan Siman Bitrus, wanda yake bayansa, ya iso ya kuwa wuce cikin kabarin. Ya ga ƙyallayen lilin kwance a can,

7haka ma zanen binnewar da aka naɗe kan Yesu da shi. Zanen a naɗe yake shi kaɗai, a keɓe da lilin ɗin.

8A ƙarshe sai almajirin nan, wanda ya kai kabarin da farko, shi ma ya shiga. Ya gani ya kuma gaskata.

9(Har yanzu ba su fahimci Nassin nan da ya ce lalle ne Yesu yă tashi daga matattu ba.)

10Sai almajiran suka koma zuwa inda suke zama.

Jesus Appears to Mary Magdalene

11Maryamu kuwa ta tsaya a bakin kabarin daga waje tana kuka. Da tana cikin kuka, sai ta sunkuya ta leƙa cikin kabarin,

12sai ta ga waɗansu mala’iku biyu saye da fararen tufafi, zaune a inda dā gawar Yesu take, ɗaya wajen kai ɗayan kuma wajen ƙafafu.

13Suka tambaye ta cewa, “Mace, don me kike kuka?”

14Da ta faɗin haka, sai ta juya ta ga Yesu tsaye, sai dai ba tă gane cewa Yesu ne ba.

15Sai ya ce, “Mace, don me kike kuka? Wa kike nema?”

16Yesu ya ce mata, “Maryamu.”

17Yesu ya ce, “Kada ki riƙe ni, gama ban riga na koma wajen Uba tukuna ba. A maimako, ki tafi wajen ’yan’uwana ki gaya musu, ‘Ina komawa wajen Ubana da Ubanku, wajen Allahna da kuma Allahnku.’ ”

18Sai Maryamu Magdalin ta wajen almajiran da labari cewa, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma gaya musu cewa ya faɗa mata waɗannan abubuwa.

Jesus Appears to the Disciples

19Da Yamman ranar farko ta mako, sa’ad da almajiran suna tare, ƙofofi kuma suna a kulle saboda tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!”

20Bayan ya faɗa haka, sai ya nuna musu hannuwansa da gefensa. Sai almajiran suka yi farin ciki ƙwarai da suka ga Ubangiji.

21Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama tă kasance tare da ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma ina aikan ku.”

22Da wannan sai ya hura musu numfashinsa ya ce, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki.

23Duk wanda kuka gafarta wa zunubansa, an gafarta masa ke nan. Duk wanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta masa ba ke nan.”

The Doubt and Faith of Thomas

24Toma kuwa (wanda ake kira Didaimus), ɗaya daga cikin Sha Biyun, ba ya tare da almajiran sa’ad da Yesu ya zo.

25Saboda haka sauran almajiran suka ce masa, “Ai, mun ga Ubangiji!”

26Bayan mako guda, har wa yau almajiransa suna cikin gidan, Toma kuwa yana tare da su. Ko da yake ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!”

27Sa’an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsarka nan; dubi hannuwana. Miƙa hannunka ka sa a gefena. Ka daina shakka ka gaskata.”

28Toma ya ce masa, “Ya Ubangijina da Allahna!”

29Sai Yesu ya ce masa, “Wato ka gaskata saboda ka gan ni ne, masu albarka ne waɗanda ba su gan ni ba, amma suka gaskata.”

30Yesu ya yi waɗansu abubuwan banmamaki da yawa a gaban almajiransa da ba a rubuta a wannan littafi ba.

31An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa.

个人灵修·旧约/诗篇

잠언 17

打开经文 →
第17章

Avoid Strife and Pursue Harmony

1Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru

2Bawa mai hikima zai yi mulki a kan da mai rashin kunya,

3Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta,

4Mugun mutum kan mai da hankali ga mugayen leɓuna;

5Duk wanda yake wa matalauta ba’a yana zagin Mahaliccinsu ne;

6Jikoki rawanin tsofaffi ne,

7Leɓunan basira ba su dace da wawa ba,

8Cin hanci kamar sihiri yake ga wanda yake ba da shi;

9Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne,

10Tsawata kan sa mutum ya koyi basira

11Mugayen mutane sukan kuta tawaye da Allah;

12Gara a haɗu da beyar da aka ƙwace wa ’ya’ya

13In mutum ya sāka alheri da mugunta,

14Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne,

15Baratar da mai laifi a kuma hukunta mai adalci,

16Mene ne amfanin kuɗi a hannun wawa,

17Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe,

18Mutumin da ba shi da azanci yakan ɗauki lamunin wani

19Duk mai son faɗa yana son zunubi,

20Mutum mai muguwar zuciya ba ya cin gaba;

21Kasance da wawa kamar ɗa yakan kawo baƙin ciki

22Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau,

23Mugun mutum yakan karɓa cin hanci a asirce

24Mutum mai basira kan kafa idonsa a kan hikima,

25Da yake wawa yakan kawo baƙin ciki ga mahaifinsa

26Ba shi da kyau a hukunta marar laifi,

27Mutum mai sani yakan yi la’akari da amfani da kalmomi,

28Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne,

个人灵修·新约

빌립보서 4

打开经文 →
第4章

Stand Firm in the Lord and Be of the Same Mind

1Saboda haka ’yan’uwana, ku da nake ƙauna, nake kuma marmarin ganinku, ku da kuke farin cikina da kuma rawanina, ku dāge ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna!

2Ina roƙon Yuwodiya ina kuma roƙon Sintike, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne.

3I, ina kuma roƙonka, abokin famata, ka taimaki matan nan waɗanda suka yi fama aikin bishara tare da ni, haka ma Kilemen da kuma sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suna cikin littafin rai.

Rejoice Always, Turn Anxiety into Prayer

4Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki!

5Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa.

6Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya.

7Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

Think on Whatever Is True and Honorable

8A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan.

9Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.

The Secret of Contentment and God Who Supplies Every Need

10Na yi farin ciki sosai ga Ubangiji don yanzu kun sāke nuna kun kula da ni. Ko da yake dā ma kun kula da ni sai dai ba ku sami dama ku nuna mini ba.

11Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali.

12Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara.

13Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

14Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina.

15Ban da haka, kamar yadda ku Filibbiyawa kuka sani, a farkon kwanakin da kuka ji bishara, sa’ad da na tashi daga Makidoniya, babu wata ikkilisiyar da tă yi tarayya da ni a fannin bayarwa da karɓa, sai ku kaɗai;

16gama ko sa’ad da nake a Tessalonika ma, kun aiko mini da taimako sau da sau sa’ad da nake cikin bukata.

17Ba cewa ina neman kyauta ba ne, sai dai ina neman abin da za a ƙara a kan ribarku.

18An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai.

19Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.

20Ɗaukaka ta tabbata ga Allahnmu da Ubanmu har abada abadin. Amin.

Final Greetings and the Blessing of Grace

21Ku gai da dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu.

22Dukan tsarkaka suna gaishe ku, musamman waɗanda suke na gidan Kaisar.

23Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku. Amin.