繁
KO 韓語
EN 英語
CN 中文
JP 日語
PH 菲律賓語系
HI 印地語
BN 孟加拉語
TA 坦米爾語
TE 泰盧固語
ML 馬拉雅拉姆語
FA 波斯語
MY 緬甸語
NE 尼泊爾語
MR 馬拉地語
KN 坎那達語
HA 豪薩語
YO 約魯巴語
SW 斯瓦希里語
IG 伊博語
ID 印尼語
PT 葡萄牙語
VI 越南語
AR 阿拉伯語
RU 俄語
UK 烏克蘭語
RO 羅馬尼亞語
IT 義大利語
FI 芬蘭語
TO 東加語
HR 克羅埃西亞語
SR 塞爾維亞語
TR 土耳其語
HU 匈牙利語
PL 波蘭語
SK 斯洛伐克語
LA 拉丁語
NL 荷蘭語
CS 捷克語
FR 法語
ES 西班牙語
DE 德語
OT 其他語言
讀經確認
你完成了這一天的麥琴讀經嗎?
點選確認後,會在我的頁面麥琴進度表中記錄為已完成。
사무엘하 23
The Last Words of David
1Waɗannan su ne kalmomin Dawuda na ƙarshe.
2“Ruhun Ubangiji ya yi magana ta wurina;
3Allah na Isra’ila ya yi magana,
4yana kama da hasken safiya
5“Ashe, gidana bai daidaita da Allah ba?
6Amma za a jefar da masu mugunta duka kamar ƙayayyuwan
7Duk wanda ya taɓa ƙaya
David's Mighty Men
8Waɗannan su ne sunayen jarumawan Dawuda.
9Na biye da shi a matsayi cikin jarumawa ukun nan, shi ne Eleyazar ɗan Dodo, mutumin Aho. Eleyazar ya kasance tare da Dawuda sa’ad da suka fuskanci Filistiyawa waɗanda suka taru a Fas Dammim don yaƙi. Mutanen Isra’ila suka gudu,
10amma ya yi tsayi daka, ya bugi Filistiyawa sai da hannunsa ya gaji har ya liƙe wa māshinsa. Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara a ranar. Sauran sojoji suka komo wurin Eleyazar, don kawai su washe ganima.
11Na biye da Agiyi a matsayi, shi ne Shamma ɗan Agi, mutumin Harar. Sa’ad da Filistiyawa suka taru a wani wurin da take gona cike da waken barewa, sai rundunar Isra’ila suka gudu daga Filistiyawa.
12Amma Shamma ya yi tsayi daka a tsakiyar gonar. Ya kāre ta, ya kuma bugi Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara.
13A lokacin girbi, uku daga cikin shugabanni talatin suka gangaro zuwa wurin Dawuda a kogon Adullam. A lokacin kuwa sojojin Filistiyawa sun kafa sansani a Kwarin Refayim.
14Dawuda kuwa yana a mafaka. Wata ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuma suna Betlehem.
15Dawuda ya ji ƙishirwa, sai ya ce, “Kash, da a ce wani yă samo mini ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem mana!”
16Sai jarumawa ukun nan suka yi kukan ƙura, suka sheƙa a guje suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka ɗebo ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda ya ƙi yă sha; a maimako sai ya zuba shi a gaban Ubangiji.
17Sai ya ce, “Ubangiji yă sawwaƙe, in yi sha! Ba jinin mutanen da suka tafi a bakin ransu ba ne?” Dawuda kuwa bai sha ruwan ba.
18Abishai, ɗan’uwan Yowab, ɗan Zeruhiya shi shugaban Ukun nan. Ya ɗauki māshinsa ya kashe mutane ɗari uku, ta haka ya zama sananne kamar Ukun nan.
19Ashe, ba a girmama shi fiye da Ukun ba? Ya zama komandansu, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba.
20Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki.
21Ya kuma buge wani jibgaggen mutumin Masar. Duk da māshin da mutumin Masar yana riƙe a hannunsa, Benahiya ya kai masa hari da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannunsa, ya kuma kashe shi da māshin.
22Irin nasarorin da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma jarumi ne sosai kamar jarumawan nan uku.
23Aka fi ba shi girma fiye da talatin ɗin nan, amma ba ya cikin ukun. Dawuda ya sa shi yă zama ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.
24Cikin talatin ɗin kuwa akwai,
25Shamma, mutumin Harod,
26Helez, mutumin Falti,
27Abiyezer, mutumin Anatot, da
28Zalmon, mutumin Aho,
29Heleb, ɗan Ba’ana daga Netofa,
30Benahiya, mutumin Firaton,
31Abi-Albon, mutumin Arba, da
32Eliyaba, mutumin Sha’albo,
33ɗan Shamma mutumin Harar,
34Elifelet, ɗan Ahasbai mutumin Ma’aka,
35Hezro, mutumin Karmel,
36Igal, ɗan Natan mutumin Zoba,
37Zelek, mutumin Ammon
38Ira, mutumin Itra.
39da kuma Uriya, mutumin Hitti.
갈라디아서 3
The Spirit Received Not by the Law
1Ya ku Galatiyawa marasa azanci! Wa ya ruɗe ku? A idanunku aka bayyana Yesu Kiristi gicciyeyye a sarari.
2Zan so in san abu guda tak daga gare ku. Kun karɓi Ruhu ta wurin kiyaye Doka ne, ko kuwa ta wurin gaskata abin da kuka ji?
3Ashe, rashin azancinku har ya kai ga haka? Bayan kun fara da Ruhu, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku ƙarasa?
4Ashe, wahaloli dabam-dabam da kuka sha sun zama a banza ke nan? Haka zai yiwu kuwa?
5Allah ya ba ku Ruhunsa yana kuma aikata ayyukan banmamaki a cikinku saboda kuna kiyaye Doka ne, ko kuwa domin kuna gaskatawa abin da kuka ji ne?
Abraham's Faith and the Curse of the Law
6Ku dubi Ibrahim mana, “Ya gaskata Allah, aka kuwa lissafta wannan adalci ne a gare shi.”
7Ku sani fa, waɗannan waɗanda suka gaskata, ’ya’yan Ibrahim ne.
8Nassi ya hanga cewa Allah zai kuɓutar da Al’ummai ta wurin bangaskiya, ya kuwa sanar wa Ibrahim wannan bisharar tun kafin lokaci yă yi cewa, “Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinka.”
9Saboda haka waɗanda suke da bangaskiya sun sami albarka tare da Ibrahim, mutumin bangaskiya.
10Dukan waɗanda suka dogara ga kiyaye Doka la’anannu ne, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda bai ci gaba da yi dukan abubuwan da aka rubuta a Littafin Doka ba.”
11A fili yake ba wanda zai kuɓuta a gaban Allah ta wurin Doka, domin “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”
12Doka ba tă dangana ga bangaskiya ba; a maimakon haka, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”
13Kiristi ya fanshe mu daga la’anar Doka ta wurin zama la’ana saboda mu, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda aka rataye a kan itace.”
14Ya fanshe mu domin albarkar da aka yi wa Ibrahim yă zo ga Al’ummai, ta wurin Kiristi Yesu, domin ta wurin bangaskiya mu karɓi alkawarin Ruhu.
The Promise Precedes the Law
15’Yan’uwa, bari in yi muku misali da rayuwarmu ta yau da kullum. Kamar dai yadda ba mai kawarwa ko yă ƙara wani abu cikin alkawarin da mutane suka kafa, haka yake a wannan batu.
16Alkawaran nan fa ga Ibrahim ne aka faɗa da kuma wani zuriyarsa. Nassi bai ce, “da zuriyoyi ba” wanda ya nuna kamar mutane da yawa, amma “ga zuriyarka,” wanda yake nufin mutum ɗaya, wanda shi ne Kiristi.
17Abin da nake nufi shi ne, Dokar da aka shigar ita bayan shekaru 430, ba tă kawar da alkawarin da Allah ya yi tun dā ba.
18Gama da a ce gādon yă dangana a kan doka ne, ai, da ba zai dangana a kan alkawari ba; amma Allah cikin alherinsa ya ba wa Ibrahim gādon ta wurin alkawari.
19To, don me aka kawo Doka? An yi ƙari da Doka ne don fitowa da laifi fili har kafin na zuriyan nan ya zo, wanda aka yi wa alkawarin, an ba da doka ta wurin mala’iku ne, aka kuma danƙa ta a hannun matsakanci.
20Kuma akan bukaci wani a tsakani ne idan da mutum biyu ake zance, Allah kuwa ɗaya ne.
21To, Dokar ce tana gāba da alkawaran Allah ke nan? Sam, ko kaɗan! Gama da a ce an ba da Dokar da tana iya ba da rai, tabbatacce, da sai a sami adalci ta wurin Doka.
22Amma Nassi ya kulle kome a ƙarƙashin ikon zunubi, domin abin da aka yi alkawarin nan, da ake bayar ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi, a ba da shi ga waɗanda suka gaskata.
Children of God Through Faith
23Kafin bangaskiyan nan tă zo, mun kasance a daure a kurkuku a ƙarƙashin Doka, a kulle sai da bangaskiyar da za tă zo ta bayyana.
24Ta haka aka sa Dokar ta zama jagorarmu zuwa ga Kiristi don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya.
25Yanzu da bangaskiya ta zo, ba sauran zamanmu a ƙarƙashin Doka.
26Dukanku ’ya’yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu.
27Gama dukanku da aka yi muku baftisma cikin Kiristi, kuna sanye da Kiristi ke nan.
28Babu bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, bawa da ’yantacce, namiji da ta mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Kiristi Yesu.
29In kuwa ku na Kiristi ne, to, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda kuma bisa ga alkawarin nan.
에스겔 30
The Day of the Lord Coming Upon Egypt
1Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2“Ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
3Gama ranar ta yi kusa,
4Takobi zai zo a kan Masar,
5Kush da Fut, Lidiya da dukan Arabiya, Libiya da kuma mutanen ƙasar alkawari za su mutu ta wurin takobi tare da Masar.
6“ ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa,
7Za su zama kango
8Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji,
9“ ‘A wannan rana manzanni za su fito daga wurina a jiragen ruwa don su tsorata Kush daga sake jikinta. Azaba za tă kama su a ranar hallakar Masar, gama tabbatacce za tă zo.
10“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
11Shi da sojojinsa, mafi bantsoro cikin al’ummai,
12Zan kafe rafuffukan Nilu
13“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
14Zan lalace Masar ta Bisa
15Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum,
16Zan ƙuna wuta wa Masar;
17Samarin Heliyofolis da Bubastis
18Duhu ne zai zama rana a Tafanes
19Ta haka zan zartar da hukunci a kan Masar,
The Prophecy of Pharaoh's Broken Arm
20A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na fari a rana ta goma sha bakwai, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
21“Ɗan mutum, na karye hannun Fir’auna sarkin Masar. Ba a daure shi don warkarwa ba ko a sa tsinke saboda kada yă zama da ƙarfi har ya riƙe takobi.
22Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da Fir’auna sarkin Masar. Zan karye hannuwansa biyu, hannun da yake da kyau da kuma wanda an riga an karya, in kuma sa takobi ya fāɗi daga hannunsa.
23Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe.
24Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon in kuma sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir’auna, zai kuwa yi nishi a gabansa kamar mutumin da aka yi wa raunin mutuwa.
25Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon, amma hannuwan Fir’auna za su shanye. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na sa takobi a hannun sarkin Babilon na kuma miƙa shi a kan Masar.
26Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”
시편 78:38-72
38Duk da haka ya kasance mai jinƙai;
39Ya tuna cewa su naman jiki ne kawai,
40Sau da yawa sun tayar masa a cikin hamada
41Sau da sau suka riƙa gwada Allah;
42Ba su tuna da ikonsa,
43ranar da ya nuna mu’ujizansa a Masar
44Ya mai da kogunansu suka zama jini;
45Ya aika da tarin ƙudajen da suka cinye su,
46Ya ba da hatsinsu ga fāra,
47Ya lalace inabinsu da ƙanƙara
48Ya miƙa shanunsu ga ƙanƙara,
49Ya saki musu fushinsa mai zafi,
50Ya shirya hanya wa fushinsa;
51Ya bugi kowane ɗan fari na Masar,
52Amma ya fitar da mutanensa kamar garke;
53Ya bi da su lafiya ƙalau, don kada su ji tsoro;
54Ta haka ya kawo su iyakar ƙasa mai tsarki,
55Ya kori al’ummai a gabansu
56Amma suka gwada Allah
57Kamar kakanninsu suka zama marasa biyayya da marasa aminci,
58Suka ba shi haushi da masujadansu na kan tudu;
59Sa’ad da Allah ya ji su, ya yi fushi ƙwarai;
60Ya yashe tabanakul na Shilo,
61Ya aika da akwatin alkawarin ƙarfinsa zuwa bauta,
62Ya ba da mutanensa ga takobi;
63Wuta ta cinye matasansu maza,
64aka karkashe firistocinsu,
65Sa’an nan Ubangiji ya farka sai ka ce daga barcinsa,
66Ya kori abokan gābansa;
67Sa’an nan ya ƙi tentunan Yusuf,
68amma ya zaɓi kabilar Yahuda,
69Ya gina wurinsa mai tsarki kamar bisa,
70Ya zaɓi Dawuda bawansa
71daga kiwon tumaki ya kawo shi
72Dawuda kuwa ya zama makiyayinsu da mutuncin zuciya;