麥克謙聖經旅程

麥克謙一年通讀

每天 4 段經文,一年讀完舊約 1 次、新約與詩篇 2 次。

365 一年固定通讀表
4 每天 4 段經文
274 選取的日次
‹ 第 274 天 / 共 365 天 ›
譯本

讀經確認

你完成了這一天的麥琴讀經嗎?

點選確認後,會在我的頁面麥琴進度表中記錄為已完成。

家庭崇拜 · 舊約

열왕기상 3

開啟正文 →
第 3 章

Solomon Marries Pharaoh's Daughter

1Solomon ya haɗa kai da Fir’auna sarkin Masar, ya kuwa auri ’yarsa. Ya kawo ta cikin Birnin Dawuda kafin yă gama ginin fadarsa, da haikalin Ubangiji, da kuma katanga kewaye da Urushalima.

2A lokacin dai mutane suna miƙa hadaya a wurare a bisa tuddai, domin ba a riga an gina haikali saboda Sunan Ubangiji ba.

3Solomon ya ƙaunaci Ubangiji ta wurin yin tafiya bisa ga farillan mahaifinsa Dawuda, sai dai ya miƙa hadayu, ya kuma ƙone turare a wuraren nan na bisa tuddai.

Solomon Asks for Wisdom at Gibeon

4Sai sarki Solomon ya tafi Gibeyon don yă miƙa hadayu, gama a can ne wuri mafi muhimmanci na sujada. Solomon kuwa ya miƙa hadayun ƙonawa guda dubu a kan wannan bagade.

5A Gibeyon, Ubangiji ya bayyana ga Solomon da dare a mafarki, Allah ya ce, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”

6Solomon ya amsa ya ce, “Ka nuna alheri mai girma ga bawanka, mahaifina Dawuda domin ya yi aminci gare ka da adalci, ya kuma kasance da zuciya mai gaskiya. Ka ci gaba da wannan alheri mai girma gare shi, ka ba shi ɗa don yă zauna a kujerar sarautarsa a wannan rana.

7“Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka sa bawanka a wurin mahaifina Dawuda. Amma ni ɗan yaro ne kawai, ban kuma san yadda zan yi ayyukana ba.

8Bawanka yana nan a cikin mutanen da ka zaɓa, mutane masu girma, waɗanda suka wuce ƙirge, ko a lissafta.

9Saboda haka ka ba bawanka zuciyar ganewa, don yă shugabanci mutanenka, yă kuma iya rarrabe tsakanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Gama wa zai iya shugabance wannan mutanenka masu girma haka?”

10Sai Ubangiji ya ji daɗi cewa Solomon ya roƙa wannan.

11Saboda haka Allah ya ce masa, “Da yake ka nemi wannan ne, ba ka kuwa nemi tsawon rai ko arziki wa kanka ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, amma ka nemi ganewa a aikata gaskiya,

12zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba.

13Ban da haka ma, zan ba ka abin da ba ka nema ba; arziki da girma, don a rayuwarka ba za ka kasance da wani kamar ka ba a cikin sarakuna.

14In kuma ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi biyayya da farillaina da umarnaina kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, zan ba ka tsawon rai.”

15Sai Solomon ya farka, ya gane ashe mafarki ne.

Solomon's Wise Judgment Between Two Women

16To, ana nan sai waɗansu karuwai biyu suka zo wurin sarki, suka tsaya a gabansa.

17Sai ɗaya ta ce, “Ranka yă daɗe, wannan mata da ni muna zama a gida ɗaya. Na haifi jariri yayinda take can tare da ni.

18Kwana uku bayan haihuwar jaririna, wannan mata ma ta haifi jariri. Mu dai kaɗai ne; babu wani a gidan sai mu biyu.

19“Da dare ɗan wannan matan ya mutu domin ta kwanta a kansa.

20Saboda haka ta tashi da tsakar dare ta ɗauki ɗana daga gefena yayinda baiwarka take barci. Sai ta sa shi kusa da ƙirjinta, ta kuma sa mataccen ɗanta kusa da ƙirjina.

21Kashegari, da na farka don in shayar da ɗana, sai na tarar ya mutu! Amma sa’ad da na dube shi da kyau da safe, sai na ga ashe ba ɗan da na haifa ba ne.”

22Amma ɗaya matar ta ce, “A’a! Mai rai ɗin ne ɗana; mataccen naki ne.”

23Sarki ya ce, “Wannan ta ce, ‘Ɗana ne a raye, naki ne matacce,’ yayinda ɗayan tana cewa, ‘A’a! Ɗanki ne mataccen, nawa ne a raye.’ ”

24Sai sarki ya ce, “Kawo mini takobi.” Sai aka kawo takobi wa sarki.

25Ya ba da umarni ya ce, “Yanka yaron nan mai rai, gida biyu, kowacce ta ɗauki rabi.”

26Ainihin mamar ɗan da yake a raye ta cika da tausayi saboda ɗanta, sai ta ce wa sarki, “Ina roƙonka, ranka yă daɗe, kada ka kashe yaron! Ka ba ta kawai!”

27Sai sarki ya zartar da hukuncinsa ya ce, “A ba da jariri mai ran ga mata ta fari. Kada a kashe shi; ita ce ainihin mahaifiyarsa.”

28Sa’ad da dukan Isra’ila suka ji hukuncin da sarki ya zartar, suka girmama sarki sosai, domin sun gane cewa Allah ya ba shi hikimar yin shari’ar adalci.

家庭崇拜 · 新約

에베소서 1

開啟正文 →
第 1 章

Greeting

1Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu,

2Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

Spiritual Blessings in Christ

3Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama.

4Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa.

5A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri.

6Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne.

7A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah

8wanda ya ba mu babu iyaka tare da dukan hikima da fahimta.

9Allah ya yi abin da ya nufa, ya kuma sanar mana shirin asirin da ya riga ya shirya yă cika ta wurin Kiristi.

10Nufinsa ke nan, idan lokaci ya cika, yă harhaɗa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikon Kiristi, wato, dukan abubuwan da suke sama da abubuwan da suke ƙasa.

11A cikinsa ne kuma aka zaɓe mu mu sami gādo daga Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi.

12Manufar Allah ita ce cewa mu da muka fara sa bege a cikin Kiristi, mu yi zaman yabon ɗaukakar Allah.

13An kuma haɗa ku a cikin Kiristi lokacin da kuka ji saƙon nan na gaskiya, wanda yake labari mai daɗi na cetonku. Da kuka ba da gaskiya, sai aka yi muku alamar shaida a cikinsa da Ruhu Mai Tsarki.

14Ruhu Mai Tsarkin nan shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari, har ya sa muka sani nan gaba Allah zai ceci waɗanda suke nasa. Wannan kuwa domin yabon ɗaukakarsa ne.

Prayer for Spiritual Wisdom

15Saboda haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan mutanen Allah,

16ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin addu’o’ina.

17Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhun hikima da na ganewa, domin ku san shi da kyau.

18Ina kuma addu’a cewa zuciyarku tă waye don ku gane ko mene ne sa zuciyan nan da ya kira ku a kansa, ku kuma san darajar dukiyan nan wadda take ta mutanen Allah, wato, albarkunsa.

19Ina addu’a ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali, wanda yake namu. Ikon da yake aiki a cikinmu, ɗaya ne da ikon nan

20da ya tā da Kiristi daga matattu, ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya.

21Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa.

22Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma ba shi iko a kan kome don amfanin ikkilisiya.

23Kuma ikkilisiya ce jikinsa; ta kuma cika da Kiristi, wanda ya cika kome ta kowace hanya.

個人靈修 · 舊約/詩篇

에스겔 34

開啟正文 →
第 34 章

Rebuke of the Shepherds Who Did Not Tend the Flock

1Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

2“Ɗan mutum, ka yi annabci a kan makiyayan Isra’ila; ka yi annabci ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kaiton makiyayan Isra’ila waɗanda suke kula da kansu ne kawai! Ashe, bai kamata makiyaya ne su lura da tumaki ba?

3Kuna cin kitsensu, kuna yi wa kanku tufafi da gashinsu, kukan yanka turkakkun, amma ba ku yi kiwon tumakin ba.

4Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ko ku warkar da marasa lafiya ko ku ɗaura waɗanda suka ji rauni. Ba ku dawo da waɗanda suka yi makuwa ko ku nemi waɗanda suka ɓace ba. Amma sai kuka mallake su ƙarfi da yaji.

5Saboda haka suka warwatse domin babu makiyayi, kuma da suka warwatsu sai suka zama abincin namun jeji.

6Tumakina suna ta yawo a kan dukan duwatsu da kuma kowane tudu. Sun watsu a dukan duniya, kuma ba wanda ya neme su.

7“ ‘Saboda haka, ku makiyaya, ku ji maganar Ubangiji,

8Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, domin tumaki sun rasa makiyayi ta haka aka washe su suka kuma zama abincin dukan namun jeji, kuma domin makiyayana ba su nemi tumakina ba amma suka kula da kansu a maimakon tumakina,

9saboda haka, ya ku makiyaya, ku ji maganar Ubangiji,

10Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da makiyaya kuma zan nemi hakkin tumakina daga gare su. Zan hana su yin kiwon tumakin don kada makiyayan su ƙara yin kiwon kansu. Zan ƙwace tumakina daga bakunansu, ba kuwa za su ƙara zama abincinsu.

The Shepherd Who Will Himself Seek and Feed the Flock

11“ ‘Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ni kaina zan nemi tumakina.

12Kamar yadda makiyayi yakan lura da tumakinsa da suka watse sa’ad da yake tare da su, haka zan lura da tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu.

13Zan dawo da su daga al’ummai in kuma tattara su daga ƙasashe, zan kuma kawo su cikin ƙasarsu. Zan yi kiwonsu a kan duwatsun Isra’ila, a maɓulɓulai da kuma cikin wuraren zamansu a ƙasar.

14Zan kula da su a wurin kiwo mai kyau, kuma ƙwanƙolin duwatsun Isra’ila ne zai zama wurin kiwonsu. Za su kwanta a wurin kiwo mai kyau, a can kuma za su yi kiwo a wurin kiwo mai kyau a kan duwatsun Isra’ila.

15Ni kaina zan lura da tumakina in kuma sa su kwanta, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

16Zan nemi ɓatattuna in kuma dawo da waɗanda suka yi makuwa. Zan ɗaura raunin waɗanda suka ji ciwo in kuma ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafa da kuma masu ƙiba. Zan yi kiwo tumaki da adalci.

17“ ‘Game da ku, tumakina, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya, da tsakanin raguna da awaki.

18Bai isa ba a ce kun yi kiwo a wuri mai kyau? Sai kun tattake sauran wurin kiwonku da ƙafafunku tukuna? Bai isa ba a ce kun sha ruwa mai tsabta? Sai kun kuma gurɓata sauran da ƙafafunku?

19Dole ne tumakina su ci abin da kuka tattake su kuma sha abin da kuka gurɓata da ƙafafunku?

20“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce musu, duba, ni kaina zan hukunta tsakanin turkakkun tumaki da ramammun tumaki.

21Domin kun tunkuɗe marasa ƙarfi da kafaɗunku, kun kuma tunkuye su da ƙahoninku sai da suka gudu,

22zan cece tumakina ba za su ƙara zama ganima ba. Zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya.

One Shepherd, David, and a Covenant of Peace

23Zan sa musu makiyaya guda, bawana Dawuda, zai kuwa lura da su; zai kula da su ya kuma zama makiyayinsu.

24Ni Ubangiji zan zama Allahnsu, bawana kuma Dawuda zai zama yerima a cikinsu. Ni Ubangiji na faɗa.

25“ ‘Zan yi alkawarin salama da su in kuma kawar wa ƙasar da namun jeji domin su zauna a hamada su kuma kwana a kurmi lafiya lau.

26Zan albarkace su in kuma sa tuduna kewaye da su. Zan zubo yayyafi a lokacinsa; za a kasance da yayyafin albarka.

27Itatuwan gona za su ba da ’ya’yansu, ƙasa kuma za tă ba da amfaninta; mutane za su zauna lafiya a ƙasarsu. Za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na karya karkiyarsu, na cece su daga hannun waɗanda suka bautar da su.

28Ba za su ƙara zama ganimar al’ummai ba, ba kuwa namun jeji za su cinye su ba. Za su zauna lafiya, kuma babu wani da zai sa su ji tsoro.

29Zan tanada musu ƙasar da aka sani don hatsinta, ba za su kuma ƙara zama abin da yunwa za tă fara musu a ƙasa ba ko su sha zargin sauran al’ummai.

30Sa’an nan za su san cewa ni, Ubangiji Allahnsu, ina tare da su kuma cewa su, gidan Isra’ila, mutanena ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

31Ku tumakina, tumakin wurin kiwona, mutanena ne, ni kuwa Allahnku ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”

個人靈修 · 新約

시편 83, 84

開啟正文 →
第 83 章

An Appeal Against United Adversaries

1Ya Allah, kada ka yi shiru;

2Dubi yadda abokan gābanka suke fariya,

3Da wayo suna ƙulle-ƙulle a kan mutanenka;

4Suna cewa, “Ku zo, bari mu hallaka su ɗungum a matsayin al’umma,

5Da zuciya ɗaya suka yi ƙulle-ƙulle tare;

6tentunan Edom da na mutanen Ishmayel,

7Gebal, Ammon da Amalek,

8Har Assuriya ma ta haɗa kai da su

9Ka yi musu abin da ka yi wa Midiyan,

10waɗanda suka hallaka a En Dor

11Ka mai da manyansu kamar Oreb da Zeyib,

12waɗanda suka ce, “Bari mu mallaki

13Ka mai da su kamar ɗan tsiron da kan karye, iska ta yi ta turawa, ya Allahna,

14kamar yadda wuta ke cin kurmi

15haka za ka kore su da iska mai ƙarfi

16Ka rushe fuskokinsu da kunya

17Bari su kasance cikin kunya da taƙaici;

18Bari su san cewa kai, wanda sunansa ne Ubangiji,

第 84 章

A Pilgrim Longing for the Lord's Courts

1Ina misalin kyan wurin zamanka,

2Raina yana marmari, har yana suma,

3Har tsada ma ta sami gida,

4Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka;

5Masu albarka ne waɗanda ƙarfinsu yana daga gare ka,

6Yayinda suke wuce ta Kwarin Baka,

7Suna ta ƙara ƙarfi,

8Ka ji addu’ata, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki;

9Ka dubi garkuwarmu, ya Allah;

10Rana guda a filayen gidan sun fi

11Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa;

12Ya Ubangiji Maɗaukaki,