M'Cheyne Bible Journey

Bible Reading Plan — M'Cheyne One Year

Follow this Bible Reading Plan through four passages a day—the Old Testament once and the New Testament and Psalms twice a year.

365 Fixed one-year plan
4 Four readings a day
271 Selected day
‹ Day 271 / 365 Today ›
Version

Reading confirmation

Did you finish this M'Cheyne day?

Confirm it to mark this day complete on your M'Cheyne progress chart.

Family · Old Testament

사무엘하 24

Open in reader →
Chapter 24

David's Census and Its Punishment

1Fushin Ubangiji ya sāke ƙuna a kan Isra’ila, sai ya zuga Dawuda, yana cewa, “Je ka ƙidaya Isra’ila da Yahuda.”

2Saboda haka sarki ya ce wa Yowab da komandodin da suke tare da shi, “Tafi cikin dukan kabilan Isra’ila, daga Dan har zuwa Beyersheba, ku ƙidaya mayaƙa don in san yawansu.”

3Amma Yowab ya ce wa sarki, “Ubangiji Allahnka ya sa mayaƙan su ƙaru sau ɗari fiye da yadda suke, har ranka yă daɗe, sarki yă gani da idonsa. Me ya sa ranka yă daɗe, sarki yake so yă yi abu haka?”

4Duk da haka, maganar sarki ya rinjayi Yowab da komandodin soja, sai suka tashi daga gaban sarki, suka tafi su ƙirga mayaƙan Isra’ila.

5Bayan suka ƙetare Urdun, sai suka yi sansani kusa da Arower, kudu da garin da yake cikin kwari, sa’an nan suka ratsa ta wajen Gad, suka ci gaba zuwa Yazer.

6Suka tafi Gileyad ta yankin Tatim Hodshi, sa’an nan suka tafi Dan Ya’an, suka kuma yi wajen kewaye Sidon.

7Sa’an nan suka yi ta wajen kagarar Taya da dukan garuruwan Hiwiyawa da Kan’aniyawa. A ƙarshe, suka ci gaba zuwa Beyersheba a Negeb na Yahuda.

8Bayan suka ratsa dukan ƙasashen, a ƙarshe suka koma Urushalima, bayan wata tara da kwana ashirin.

9Yowab ya ba wa sarki jimillar yawan mayaƙan. A Isra’ila akwai mutum dubu ɗari takwas da za su iya riƙe takobi. A Yahuda kuwa mutum dubu ɗari biyar.

10Bayan Dawuda ya ƙidaya mayaƙan, lamirinsa ya kāshe shi, sai ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji na yi laifi ƙwarai a kan abin da na yi. Ina roƙonka ka gafarta wa bawanka. Na yi wauta ƙwarai.”

11Kafin Dawuda yă tashi da safe kashegari, maganar Ubangiji ta riga ta zo wa annabin nan Gad, mai duban nan na Dawuda. Ubangiji ya ce,

12“Je ka faɗa wa Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, ina ba ka zaɓi uku. Ka zaɓi ɗaya daga cikinsu don in aikata maka shi.’ ”

13Sai Gad ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Kana so a yi yunwa shekara uku a ƙasarka? Ko kana so ka yi ta gudu a gaban abokan gābanka har wata uku? Ko kuwa ka fi so a yi annoba kwana uku a ƙasarka? Yanzu, sai ka yi tunani, ka yanke shawarar game da amsar da zan mayar wa wanda ya aiko ni.”

14Dawuda ya ce wa Gad, “Na shiga uku. Gara mu fāɗa a hannuwan Ubangiji gama alherinsa da girma yake. Amma fa kada ka bar ni in fāɗa a hannun mutane.”

15Saboda haka Ubangiji ya aika da annoba a kan Isra’ila tun daga safe har zuwa lokacin da aka ƙayyade, mutum dubu saba’in kuwa daga Dan zuwa Beyersheba suka mutu.

16Da mala’ikan Ubangiji ya miƙa hannunsa wajen Urushalima, don yă hallaka ta, sai Ubangiji ya tsai da masifar, ya ce wa mala’ikan da yake wahal da mutane, “Ya isa, ka janye hannunka.” A lokacin kuwa Mala’ikan Ubangiji yana tsaye a masussukar Arauna, mutumin Yebus.

17Da Dawuda ya ga mala’ikan da ya bubbugi mutane, sai ya ce wa Ubangiji, “Ni ne na yi zunubi, na kuma yi abin da ba daidai ba. Waɗannan tumaki ne kawai. Me suka yi? Bari hukuncinka yă sauko a kaina da iyalina.”

David Builds an Altar at the Threshing Floor of Araunah

18A ranar, Gad ya koma wurin Dawuda ya ce, “Ka tashi, ka tafi ka gina wa Ubangiji bagade a masussukar Arauna, mutumin Yebus.”

19Saboda haka Dawuda ya haura, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Gad.

20Da Arauna ya hangi Dawuda da mutanensa suna zuwa wajensa, sai ya fita a guje, ya je ya rusuna a gaban sarki.

21Arauna ya ce, “Me ya sa ranka yă daɗe, sarki ya zo wajen bawansa?”

22Arauna ya ce wa Dawuda, “Bari ranka yă daɗe, sarki yă ɗauki duk abin da ya ga dama yă miƙa shi. Ga shanu, don hadaya ta ƙonawa, ga kuma kayan masussuka da itacen shanu, don itace.”

23Dukan wannan, ranka yă daɗe, Arauna ya ba wa sarki. Arauna ya kuma ce, “Bari Ubangiji Allahnka yă karɓa.”

24Amma sarki ya ce wa Arauna, “A’a, dole in biya ka saboda waɗannan. Ba yadda zan miƙa wa Ubangiji Allahna hadayun ƙonawa da bai ci mini kome ba.”

25Dawuda ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya kuma miƙa masa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama. Sa’an nan Ubangiji ya amsa addu’o’in a madadin ƙasar, aka kuma kawar wa Isra’ila annoban.

Family · New Testament

갈라디아서 4

Open in reader →
Chapter 4

Called from Slaves to Sons

1Abin da nake nufi shi ne, muddin magāji yana ɗan yaro ne tukuna, babu bambanci tsakaninsa da bawa, ko da yake shi ne da mallakar kome.

2Yana ƙarƙashin iyayen goyonsa da masu riƙon amana har yă zuwa cikar lokacin da mahaifinsa ya sa.

3Haka yake, sa’ad da muke ’yan yara, mun kasance cikin bauta a ƙarƙashin ƙa’idodin duniya.

4Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka,

5domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ’ya’ya.

6Da yake ku ’ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake kira, “Abba, Uba.”

7Saboda haka kai ba bawa ba ne kuma, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji.

Do Not Turn Back to Weak Elemental Principles

8Dā da ba ku san Allah ba, ku bayi ne ga waɗanda a ainihi ba alloli ba ne.

9Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma a ce Allah ya san ku, yaya kuke sāke komawa ga ƙa’idodin duniya marasa ƙarfi, abin tausayi kuma? Kuna so ku sāke komawa ga bautarsu ne?

10Kuna kiyaye ranaku da watanni da lokuta da shekaru na musamman!

11Kai, kun ba ni tsoro, don ya zama kamar duk wahalar da na yi a kanku banza ne!

Paul's Heartfelt Appeal to the Galatians

12Ina roƙonku ’yan’uwa, ku zama kamar ni, gama na zama kamar ku. Ba ku yi mini wani laifi ba.

13Kun san rashin lafiyar da na yi, shi ne ya yi mini hanyar da na kawo muku bishara da farko.

14Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce mala’ikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa.

15Me ya faru da dukan farin cikinku? Na tabbata, a lokacin, da mai yiwuwa ne da kun ciccire idanunku kun ba ni.

16Yanzu na zama abokin gābanku don na faɗa muku gaskiya ke nan?

17Waɗancan mutane suna neman su rinjaye ku da ƙwazo, amma ba da kyakkyawar aniya ba. Abin da suke so shi ne su raba ku da mu, saboda ƙwazonku yă koma gare su.

18Yana da kyau ku kasance da irin wannan niyya idan da nufi mai kyau ne, ku kuma kasance a haka koyaushe ba sai ina tare da ku ba.

19Ya ku ’ya’yana ƙaunatattu, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har sai Kiristi ya kahu a cikinku.

20Da ma a ce ina tare da ku yanzu in canja muryata mana! Gama na damu ƙwarai saboda ku!

Hagar and Sarah, an Allegory of Two Covenants

21Ku gaya mini, ku da kuke so ku zauna a ƙarƙashin Doka, ba ku san abin da Doka ta ce ba ne?

22Gama a rubuce yake cewa Ibrahim yana da ’ya’ya biyu maza, ɗaya ta wurin mace ’yar aikin gidansa, ɗaya kuma ta wurin ainihin matarsa.

23Ɗansa na wajen mace ’yar aikin gidansa ya zo bisa ga ƙa’idar jiki ne; amma ɗansa na wajen ainihin matarsa ya zo a sakamakon alkawarin ne.

24Za a iya ɗaukan waɗannan al’amura a matsayin misali, domin matan nan suna misalta alkawura biyu ne. Alkawari ɗaya daga Dutsen Sinai ne yana kuma haihuwar ’ya’yan da za su zama bayi. Hagar ke nan.

25Hagar tana a matsayin Dutsen Sinai a Arabiya tana kuma kwatancin birnin Urushalima na yanzu, gama ita baiwa ce tare da ’ya’yanta.

26Amma Urushalimar da take sama ’yantacciya ce, ita ce kuma mahaifiyarmu.

27Gama a rubuce yake cewa,

28To, ku ’yan’uwa, ku ’ya’yan alkawari ne kamar Ishaku.

29A wancan lokaci, wannan ɗa wanda aka haifa ta wurin ƙa’idar jiki ya tsananta wa wanda aka haifa ta ikon Ruhu. Haka ma yake har yanzu.

30Amma me Nassi ya ce? Nassi ya ce, “Kori macen nan ’yar aikin gida da ɗanta don ɗan mace ’yar aikin gida ba zai taɓa raba gādo tare da ɗa na ainihin matarka ba.”

31Saboda haka, ’yan’uwa, mu ba ’ya’yan mace ’yar aikin gida ba ne, amma na ainihin matan gidan ne.

Secret · OT / Psalms

에스겔 31

Open in reader →
Chapter 31

Egypt Likened to a Cedar of Lebanon

1A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na uku a rana ta farko, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

2“Ɗan mutum, faɗa wa Fir’auna sarkin Masar da jama’arsa cewa,

3Ka dubi Assuriya, ta taɓa zama kamar al’ul a Lebanon

4Ruwa ya sa ya yi girma,

5Saboda haka ya yi tsayi

6Dukan tsuntsayen sararin sama

7Yana da girma a kyau,

8Al’ul a cikin lambun Allah

9Na sa ya yi kyau

The Cedar Cut Down and Brought to Sheol

10“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin ya yi tsayi, kansa kuma ya kai cikin gizagizai, kuma domin ya yi fariya saboda tsayinsa,

11na miƙa shi ga mai mulkin al’ummai, don yă sāka masa gwargwadon muguntarsa. Na jefar da shi a gefe,

12kuma baƙi mafi mugunta na al’ummai suka sare shi suka bar shi. Rassansa sun fāɗi a kan duwatsun da suke cikin dukan kwaruruka; rassansa kuma sun kakkarye, sun fāɗi a cikin dukan magudanan ruwa na ƙasa. Dukan al’umman duniya suka fito daga ƙarƙashin inuwarsa suka bar shi.

13Dukan tsuntsaye sararin sama suka zauna a itacen da ya fāɗi, dukan namun jeji kuma suna cikin rassansa.

14Saboda haka ba wani daga cikin itatuwan da suke kusa da ruwan da zai taɓa yin fariyar tsawonsa, har kawunansu su kai cikin gizagizai. Ba wani daga cikin itatuwan da ya sha ruwa sosai da zai taɓa yi wannan tsayi; duk an bashe su ga mutuwa, zuwa can ƙasa, a cikin matattu, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.

15“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da aka yi ƙasa da shi zuwa kabari na rufe zurfafa maɓulɓulai da makoki dominsa; na janye rafuffukansa, aka kuma hana yalwan ruwansa. Saboda shi na rufe Lebanon da baƙin ciki, dukan itatuwan kurmi suka bushe.

16Na sa al’ummai suka yi rawar jiki da jin ƙarar fāɗuwarsa sa’ad da na yi ƙasa da shi zuwa kabari tare da waɗanda suka gangara rami. Sai dukan itatuwan Eden, zaɓaɓɓu da kuma mafi kyau na Lebanon, dukan itatuwan da aka yi musu banruwa, sun ta’azantu a ƙarƙashin ƙasa.

17Waɗanda suka zauna a inuwarsa, dukan masu tarayyarsa a cikin al’ummai, su ma sun gangara zuwa kabari tare da shi, sun haɗu da waɗanda aka kashe da takobi.

18“ ‘Da wa cikin itatuwan Eden za a kwatanta da kai cikin girma da daraja? Duk da haka kai ma, za a yi ƙasa da kai tare da itatuwan Eden zuwa ƙarƙashin ƙasa; za ka kwanta a cikin marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi.

Secret · New Testament

시편 79

Open in reader →
Chapter 79

A Lament over the Defiled Temple

1Ya Allah, al’ummai sun mamaye gādonka;

2Sun ba da gawawwakin bayinka

3Sun zubar da jini kamar ruwa

4Mun zama abin reni ga maƙwabta,

5Har yaushe, ya Ubangiji za ka yi ta fushi? Har abada ne?

6Ka zuba fushinka a kan al’umman

7gama sun cinye Yaƙub

8Kada ka riƙe zunubai kakanni a kanmu;

9Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu,

10Don me al’ummai za su ce,

11Bari nishe-nishen ’yan kurkuku su zo gabanka;

12Ka sāka a cinyoyin maƙwabtanmu sau bakwai

13Sa’an nan mu mutanenka, tumakin makiyayarka,