VI
Ngôn ngữ trang web
Tiếng Việt VI English EN 한국어 KO Filipino FIL 日本語 JA 简体中文 简 繁體中文 繁 Español ES Français FR Deutsch DE Русский RU Português PT Italiano ITVI Tiếng Việt
Ngôn ngữ trang web
Tiếng Việt VI English EN 한국어 KO Filipino FIL 日本語 JA 简体中文 简 繁體中文 繁 Español ES Français FR Deutsch DE Русский RU Português PT Italiano ITHành trình Kinh Thánh của M'Cheyne
Kế hoạch đọc Kinh Thánh — M'Cheyne One Year
Thực hiện theo Kế hoạch đọc Kinh Thánh này qua bốn đoạn mỗi ngày—Cựu Ước một lần, Tân Ước và Thi Thiên hai lần một năm.
KO Tiếng Hàn
EN Tiếng Anh
CN Tiếng Trung
JP tiếng Nhật
PH Ngôn ngữ Philippine
HI Tiếng Hindi
BN tiếng Bengali
TA Tiếng Tamil
TE tiếng Telugu
ML Mã Lai
FA tiếng Ba Tư
MY Miến Điện
NE tiếng Nepal
MR Tiếng Marathi
KN tiếng Kannada
HA Tiếng Hausa
YO Tiếng Yoruba
SW tiếng Swahili
IG người Igbo
ID tiếng Indonesia
PT tiếng Bồ Đào Nha
VI Tiếng Việt
AR tiếng Ả Rập
RU tiếng Nga
UK tiếng Ukraina
RO người Rumani
IT người Ý
FI tiếng Phần Lan
TO tiếng Tonga
HR tiếng Croatia
SR tiếng Serbia
TR tiếng Thổ Nhĩ Kỳ
HU tiếng Hungary
PL tiếng Ba Lan
SK Tiếng Slovak
LA tiếng Latinh
NL tiếng Hà Lan
CS tiếng Séc
FR người Pháp
ES tiếng Tây Ban Nha
DE tiếng Đức
OT Ngôn ngữ khác
Xác nhận đọc
Bạn đã kết thúc ngày M'Cheyne này chưa?
Xác nhận nó để đánh dấu ngày này hoàn thành trên biểu đồ tiến độ M'Cheyne của bạn.
사무엘하 22
David's Song of Thanksgiving
1Dawuda ya rera wannan waƙa ga Ubangiji, sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa, da kuma daga hannun Shawulu.
2Ya ce,
3Allahna shi ne dutsena. A gare shi nake samun kāriya
4“Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo,
5Raƙumar ruwan mutuwa sun kewaye ni;
6Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe ni;
7“A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji;
8Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza,
9Hayaƙi ya taso daga kafaffen hancinsa;
10Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa,
11Ya hau kerubobi, ya tashi sama;
12Ya mai da duhu abin rufuwarsa
13Daga cikin hasken gabansa
14Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama;
15Ya harbe kibiyoyi, ya wartsar da abokan gāba,
16Aka bayyana kwarin teku,
17“Daga sama ya miƙo hannu ya ɗauke ni,
18Ya kuɓutar da ni daga hannun abokin gāba mai iko,
19Suka auka mini cikin ranar masifata,
20Ya fito da ni, ya kai ni wuri mafi fāɗi;
21“Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina;
22Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji;
23Dukan dokokinsa suna a gabana;
24Ba ni da laifi a gabansa
25Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina
26“Ga masu aminci, kakan nuna kanka mai aminci,
27ga masu tsarki, kakan nuna musu tsarki.
28Kakan ceci mai tawali’u,
29Ya Ubangiji kai ne fitilata;
30Da taimakonka zan iya auka wa rundunar sojoji;
31“Ga Allah dai, hanyarsa cikakkiya ce;
32Gama wane ne Allah, in ba Ubangiji ba?
33Allah ne ya ba ni ƙarfi,
34Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa;
35Ya hori hannuwana don yaƙi,
36Ka ba ni garkuwar nasararka;
37Ka fadada hanya a ƙarƙashina
38“Na fafari abokan gābana, na murƙushe su;
39Na hallaka su ƙaƙaf, ba kuwa za su ƙara tashi ba,
40Ka ba ni ƙarfi don yaƙi;
41Ka sa abokan gābana suka juya a guje,
42Suka nemi taimako, amma babu wanda zai cece su,
43Na murƙushe su, suka yi laushi kamar ƙura;
44“Ka kuɓutar da ni daga harin mutanena;
45baƙi kuma su na zuwa don su yi mini fadanci;
46Zukatansu ta karaya;
47“Ubangiji yana a raye! Yabo ta tabbata ga Dutsena!
48Shi ne Allahn da yake rama mini,
49wanda ya kuɓutar da ni daga maƙiyina.
50Saboda haka, zan yabe ka, ya Ubangiji cikin dukan al’ummai;
51“Ya ba wa sarkinsa kyakkyawan nasara;
갈라디아서 2
The Gospel to the Gentiles Affirmed by the Apostles
1Bayan shekara goma sha huɗu sai na sāke haurawa zuwa Urushalima, a wannan lokaci na tafi tare da Barnabas. Na kuma ɗauki Titus muka tafi tare.
2Na tafi ne bisa ga wani wahayi. Da na kai can, sai na bayyana musu bisharar da nake wa’azi a cikin Al’ummai. Na yi haka a keɓance a gaban waɗanda suke shugabanni, don tsoro kada gudun da nake yi, ko kuwa na riga na yi, yă zama a banza.
3Amma ko Titus ma da yake tare da ni, ba a ce dole sai ya yi kaciya ba, ko da yake shi mutumin Al’ummai ne.
4Wannan zancen kaciya ya taso domin waɗansu ’yan’uwan ƙarya sun shiga cikinmu domin su yi leƙe a kan ’yancin da muke da shi a cikin Kiristi Yesu, su kuma mai da mu bayi.
5Ba mu kuwa ba su zarafi ba ko kaɗan, don gaskiyar bishara ta ci gaba da kasance tare da ku.
6Game da waɗanda aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne, ko wane ne su, duk ɗaya ne a wurina; gama Allah ba ya nuna bambanci, ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙara mini kome ba.
7A maimakon haka, sun ga cewa an danƙa mini hakkin wa’azin bishara ga Al’ummai, kamar yadda aka danƙa wa Bitrus ga Yahudawa.
8Gama Allah wanda ya yi aiki a cikin hidimar Bitrus a matsayin manzo ga Yahudawa, haka ma ya yi aiki a cikin hidimata a matsayin manzo ga Al’ummai.
9Yaƙub, Bitrus da Yohanna waɗanda suke fitattun ginshiƙai, sun karɓe ni da Barnabas da hannu biyu biyu sa’ad da suka gane alherin da aka ba ni. Suka kuma yarda cewa ya kamata mu tafi wajen Al’ummai, su kuwa su tafi wajen Yahudawa.
10Abin da dai suka roƙa shi ne ya kamata mu riƙa tuna da matalauta, abin nan da nake marmarin yi.
Paul Rebukes Peter at Antioch
11Sa’ad da Bitrus ya zo Antiyok, na tsawata masa ido da ido don laifinsa a fili yake.
12Kafin waɗansu mutane su zo daga wurin Yaƙub, yakan ci abinci tare da Al’ummai. Amma da suka iso, sai ya fara janyewa, ya kuma ware kansa daga wajen Al’ummai domin yana tsoron waɗanda suke ƙungiyar masu kaciya.
13Sauran Yahudawa suka haɗa kai da shi a munafuncinsa har Barnabas ma ya bauɗe.
14Da na ga cewa ba sa yin daidai da gaskiyar bishara, sai na ce wa Bitrus a gabansu duka, “Kai mutumin Yahuda ne, duk da haka kana rayuwa kamar Ba’al’umme ba kamar mutumin Yahuda ba. To, yaya aka yi, kana tilasta Al’ummai su bi al’adun Yahudawa?
Justified by Faith
15“Mu da muke Yahudawa ta wurin haihuwa ba Al’ummai masu zunubi ba,
16mun san cewa mutum ba ya samun kuɓuta ta wurin kiyaye Doka, sai dai ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Saboda haka, mu ma, muka sa bangaskiyarmu cikin Kiristi Yesu don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya cikin Kiristi ba ta wurin kiyaye Doka ba, domin ba wanda zai kuɓuta ta wurin bin Doka.
17“In kuwa ya zama muna so mu sami zaman marasa laifi a gaban Allah ta wurin dogara ga Kiristi, sa’an nan an same mu mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, ko wannan zai nuna Kiristi yana ƙarfafa zunubi ke nan? A’a, ko kusa!
18In na sāke gina abin da na rushe, na zama mai karyar Doka ke nan.
19“Gama ta wurin Doka na mutu ga Doka saboda in rayu ga Allah.
20An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.
21Ba na ajiyar alherin Allah a gefe, gama da a ce ana samun adalci ta wurin Doka, ai, da Kiristi ya mutu a banza ke nan!”
에스겔 29
Judgment on Pharaoh of Egypt Like a Great Monster
1A shekara ta goma, a wata na goma, a rana ta goma sha biyu, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2“Ɗan mutum, ka fuskanci Fir’auna sarkin Masar ka kuma yi annabci gāba da shi da dukan Masar.
3Yi masa magana ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
4Amma zan sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka
5Zan bar ka a cikin hamada,
6Ta haka dukan waɗanda suke zama a Masar za su san cewa ni ne Ubangiji.
7Sa’ad da suka kama ka da hannuwansu, ka tsattsage, ka kuma buɗu a kafaɗunsu; sa’ad da suka jingina a kanka, sai ka karye, bayansu kuwa ya firgita.
8“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan kawo takobi a kanka in kashe mutane da dabbobi.
9Masar za tă zama kufai. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.
10saboda haka ina gāba da kai da rafuffukanka, zan kuma maishe ƙasar Masar ta lalace ta kuma zama kango daga Migdol zuwa Aswan, har iyakar Kush.
11Ba ƙafar mutum ko ta dabbar da za tă ratsa ta; ba wanda zai zauna a can har shekaru arba’in.
12Zan mai da ƙasar Masar kufai a cikin ƙasashen da aka ragargaza, biranenta kuma za su zama kango har shekaru arba’in a cikin biranen da aka lalace. Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe.
13“ ‘Duk da haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ƙarshen shekaru arba’in ɗin zan tattara Masarawa daga al’ummai inda aka warwatsa su.
14Zan komo da su daga zaman bauta in mai da su zuwa Masar ta Bisa, ƙasarsu ta ainihi. A can za su zama masarauta marar ƙarfi.
15Za tă zama masarauta mafi rarrauna cikin masarautai, ba kuwa za tă ƙara ɗaga kanta a kan sauran al’ummai ba. Zan sa tă zama marar ƙarfi ƙwarai, har da ba za tă ƙara yin mulkin a kan al’ummai ba.
16Masar ba za tă ƙara zama abin dogara ga mutanen Isra’ila ba amma za tă zama abin tunin zunubinsu na juyawa gare ta don taimako. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
The Land of Egypt Given to Nebuchadnezzar
17A shekara ta ashirin da bakwai, a wata na fari a rana ta farko, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
18“Ɗan mutum, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya sa sojojinsa su matsa wa Taya; kowane kai ya koɗe, kowace kafaɗa kuma ta goge. Duk da haka shi da sojojinsa ba su sami wani lada daga matsin da suka yi a kan Taya ba.
19Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan ba da Masar ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, zai washe dukiyarta. Zai kwashe ya washe ƙasar ganima a matsayin abin biyan sojojinsa.
20Saboda haka na ba shi Masar a matsayin lada don ƙoƙarinsa domin shi da sojojinsa sun yi wannan domina ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
21“A wannan rana zan sa ƙaho ya tsiro wa gidan Isra’ila, zan kuma buɗe bakinka a cikinsu. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”
시편 78:1-37
God's Deeds Handed Down to the Generations
1Ya mutanena, ku ji koyarwata;
2Zan buɗe bakina da misalai,
3abin da muka ji muka kuma sani,
4Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba;
5Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub
6don tsara na biye su san su,
7Ta haka za su dogara ga Allah
8Ba za su zama kamar kakanni kakanninsu ba,
9Mutanen Efraim, ko da yake suna da bakkuna,
10ba su kiyaye alkawarin Allah ba
11Suka manta da abin da ya aikata,
12Ya yi mu’ujizai a idanun kakanninsu
13Ya raba teku ya kuma bi da su ciki;
14Ya bishe su da girgije da rana
15Ya tsage duwatsu a cikin hamada
16ya fid da rafuffuka daga dutsen da ya tsaga
17Amma suka ci gaba da yin masa zunubi,
18Da gangan suka gwada Allah
19Suka yi magana a kan Allah,
20Sa’ad da ya bugi dutse,
21Sa’ad da Ubangiji ya ji su, ya yi fushi ƙwarai;
22gama ba su gaskata ga Allah ba
23Duk da haka ya ba da umarni ga sarari a bisa
24ya sauko da Manna wa mutanensa don su ci,
25Mutane suka ci burodin mala’iku;
26Ya saki iskar gabas daga sammai
27Ya sauko da nama a kansu kamar ƙura,
28Ya sa suka sauka a cikin sansaninsu,
29Suka ci har suka sami fiye da abin da ya ishe su,
30Amma kafin su juyo daga abincin da suka yi kwaɗayi,
31fushin Allah ya ƙuna a kansu;
32Duk da haka, suka ci gaba da yin zunubi;
33Saboda haka ya sa kwanakinsu suka ƙare a banza
34A duk sa’ad da Allah ya kashe su, sai su neme shi;
35Sun tuna cewa Allah ne Dutsensu,
36Amma sai su yi ta yin masa zaƙin baki,
37zukatansu ba sa biyayya gare shi,