scripture.how 성경필사
KO

Copywork

Hausa BSRK 에스더 7장

성경필사는 빠르게 끝내는 입력 훈련이 아니라, 한 절씩 말씀의 문장과 흐름을 다시 붙드는 시간입니다. 입력 내용은 이 브라우저에 임시 저장되며, 로그인하면 계정에도 저장됩니다.

KO 한국어
ZH 중국어
JA 일본어
HI 힌디어
BN 벵골어
TA 타밀어
TE 텔루구어
ML 말라얄람어
FA 페르시아어
MY 버마어
NE 네팔어
MR 마라티어
KN 칸나다어
HA 하우사어
YO 요루바어
SW 스와힐리어
IG 이그보어
ID 인도네시아어
TSI
PT 포르투갈어
VI 베트남어
AR 아랍어
AVD
RU 러시아어
UK 우크라이나어
RO 루마니아어
BTF
IT 이탈리아어
FI 핀란드어
TO 통가어
HR 크로아티아어
SR 세르비아어
TR 튀르키예어
HU 헝가리어
PL 폴란드어
SK 슬로바키아어
LA 라틴어
NL 네덜란드어
CS 체코어
FR 프랑스어
ES 스페인어
DE 독일어
ETC 기타 언어
7:1
대기

Saboda haka sarki da Haman suka tafi cin abinci wurin sarauniya Esta.

7:2
대기

Yayinda suke shan ruwan inabi a rana ta biyun nan, sai sarki ya sāke tambaya, “Sarauniya Esta, me kike so? Za a ba ki. Mene ne roƙonki? Ko da rabin masarautata ne, za a ba ki.”

7:3
대기

Sai Sarauniya Esta ta amsa ta ce, “In na sami tagomashi a wurinka, ya sarki, in kuma mai girma ya yarda, a bar ni da raina, wannan shi ne roƙona. Ka kuma sa kada a kashe mutanena, wannan ita ce bukata.

7:4
대기

Gama an sayar da ni da mutanena don a hallaka, a karkashe mu, a kuma ƙi mu. Da a ce an sayar da mu kamar bayi maza da mata ne, da na yi shiru, domin wannan zai zama abin da bai taka kara ya karye ba, har da za a dami sarki a kai.”

7:5
대기

Sarki Zerzes ya tambayi Sarauniya Esta ya ce, “Wane ne shi? Ina mutumin da ya yi ƙarfin halin yin wannan karambani?”

7:6
대기

Esta ta ce, “Maƙiyi da abokin gāban, shi ne wannan mugun Haman.”

7:7
대기

Sarki ya tashi cikin fushi, ya bar ruwan inabinsa, ya fita zuwa cikin lambun fada. Amma da Haman ya gane cewa sarki ya riga ya yanke shawara a kan ƙaddararsa, ya dakata domin yă roƙi sarauniya Esta saboda ransa.

7:8
대기

Sarki yana dawowa daga lambun fada zuwa babban zauren liyafan ke nan, sai ga Haman ya fāɗi a kan shimfiɗar da Esta take zaune.

7:9
대기

Sai Harbona, ɗaya daga cikin bābānni masu yi wa sarki hidima ya ce, “Akwai wurin rataye mai laifi da tsayinsa ya kai ƙafa saba’in da biyar yana nan tsaye kusa da gidan Haman. Ya gyara shi ne domin a rataye Mordekai, wanda ya yi cece sarki wanda ya tone makircin masu niyya su hallaka sarki.”

7:10
대기

Saboda haka suka rataye Haman a kan wurin rataye mai laifin da shi Haman ya shirya saboda Mordekai. Sa’an nan sarki ya huce.