scripture.how 성경필사
KO

Copywork

Hausa BSRK 말라기 2장

성경필사는 빠르게 끝내는 입력 훈련이 아니라, 한 절씩 말씀의 문장과 흐름을 다시 붙드는 시간입니다. 입력 내용은 이 브라우저에 임시 저장되며, 로그인하면 계정에도 저장됩니다.

KO 한국어
ZH 중국어
JA 일본어
HI 힌디어
BN 벵골어
TA 타밀어
TE 텔루구어
ML 말라얄람어
FA 페르시아어
MY 버마어
NE 네팔어
MR 마라티어
KN 칸나다어
HA 하우사어
YO 요루바어
SW 스와힐리어
IG 이그보어
ID 인도네시아어
TSI
PT 포르투갈어
VI 베트남어
AR 아랍어
AVD
RU 러시아어
UK 우크라이나어
RO 루마니아어
BTF
IT 이탈리아어
FI 핀란드어
TO 통가어
HR 크로아티아어
SR 세르비아어
TR 튀르키예어
HU 헝가리어
PL 폴란드어
SK 슬로바키아어
LA 라틴어
NL 네덜란드어
CS 체코어
FR 프랑스어
ES 스페인어
DE 독일어
ETC 기타 언어
2:1
대기

“Yanzu fa wannan gargaɗi dominku ne, ku firistoci.

2:2
대기

In ba ku saurara ba, in kuma ba ku sa zuciyarku ga girmama sunana ba, zan aukar muku da la’ana, zan kuma la’antar da albarkunku. I, na riga na la’anta su, domin ba ku sa zuciyarku ga girmama ni ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.

2:3
대기

“Saboda ku zan tsawata wa zuriyarku; zan watsa kashin dabbobin hadayunku a fuskokinku, a kuma kwashe ku tare da shi.

2:4
대기

Za ku kuwa san cewa ni ne na aika muku da wannan gargaɗi domin alkawarina da Lawi yă ci gaba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

2:5
대기

“Alkawarina da shi, alkawari ne na rai da salama, wanda na ba shi; domin yă girmama ni, ya kuwa girmama ni, ya kuma ji tsoron sunana ƙwarai.

2:6
대기

Umarnin gaskiya yana a bakinsa, ba a kuma sami wani ƙarya a leɓunansa ba. Ya yi tafiya tare da ni cikin salama da adalci, ya kuwa juyo da mutane masu yawa daga zunubi.

2:7
대기

“Gama ya kamata leɓunan firist su kiyaye ilimi, ya kamata kuma mutane su nemi umarni daga bakinsa, domin shi ne manzon Ubangiji Maɗaukaki.

2:8
대기

Amma sai kuka kauce hanya, ta wurin koyarwarku kuma kuka sa mutane da yawa suka yi tuntuɓe; kun keta alkawarin da na yi da Lawi,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

2:9
대기

“Saboda haka na sa a rena ku, a kuma wulaƙanta ku a gaban dukan mutane, domin ba ku bi hanyoyina ba amma kuka nuna sonkai a al’amuran shari’a.”

2:10
대기

Ashe, ba Mahaifi guda dukanmu muke da shi ba? Ba Allah ɗaya ne ya halicce mu ba? Don me muka keta alkawarin kakanninmu ta wurin cin amanar juna?

2:11
대기

Yahuda ya ci amana. An yi abin kunya a Isra’ila da kuma a Urushalima. Yahuda ya ƙazantar da wuri mai tsarkin da Ubangiji yake ƙauna, ta wurin auren ’yar wani baƙon allah.

2:12
대기

Game da mutumin da ya aikata wannan, ko wane ne shi, bari Ubangiji yă yanke shi daga tentunan Yaƙub, ko da ma ya kawo hadayu ga Ubangiji Maɗaukaki.

2:13
대기

Ga kuma wani abin da kuke yi. Kukan cika bagaden Ubangiji da hawaye. Kukan yi kuka kuna ihu gama Ubangiji ba ya mai da hankali ga hadayunku ko yă karɓe su da farin ciki.

2:14
대기

Kukan ce, “Don me ba ya karɓan hadayunmu?” Ai, domin Ubangiji ya zama shaida tsakaninka da matar ƙuruciyarka, gama ka keta amanar da ka yi mata, ko da yake ita abokiyar zamanka ce, matar aurenka ta alkawari.

2:15
대기

Ashe, Ubangiji bai maishe su ɗaya ba? Cikin jiki da ruhu, su nasa ne. Me ya sa suke ɗaya? Domin yana neman ’ya’ya masu tsoron Allah. Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amanar matar ƙuruciyarka.

2:16
대기

“Na ƙi kisan aure,” in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila. “Na kuma ƙi mutumin da ya rufe kansa da tashin hankali kamar riga,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

2:17
대기

Kun sa Ubangiji Maɗaukaki ya gaji da maganganunku.